Manufofin Turkiyya wajen taimaka dan adam da masu neman mafaka

Turkiyya ta kasance ƙasar da ake koyi da ita kasancewar yadda ta ke taimakawa bil adama da kuma irin ingantattun matakai da take dauka akan lamurkan ƴan gudun hijira.

Manufofin Turkiyya wajen taimaka dan adam da masu neman mafaka

Turkiyya dai tana koyar da duniya akan harkokin taimakawa bil adama ga sauran ƙasashen duniya. Turkiyya nada matakan da take ɗauka domin tallafawa rayuwar al'umma wanda ya banbanta da yadda wasu ƙasashen ke yi, hakan ne ya sanya Turkiyya kasancewa a kan gaba a fagen tallafawa ɗan Adam a duniya. Alƙaluman shekarar 2018 sun bayyana cewar Turkiyya ce tafi ko wacce ƙasa tallafawa ɗan adam inda take kashe kaso 0.85 cikin ɗarin kuɗaɗen shigarta domin taimakawa ɗan adam, a yayinda kasashen Luxembourg da Norway ke binta baya da kaso 0.17 cikin ɗari.

Wannan sharhin Malam Yazar Can ACUN ne daga cibiyar nazarin ilmin siyasa da tattalin arziki wato SETA.

Binciken Hukumar Ci Gaba dake ƙasar lngila ya bayyana Turkiyya wacce ke kashe dala biliyan 8.07 domin bayar da agaji a matsayar ƙasar da tafi ko wacce taimakawa ɗan adam a duniya. Amurka ce ke bin Turkiyya a baya da biliyan 6.68. Amurka na kashe kaso 0.04 cikin ɗarin kuɗaɗen shigarta domin tallafawa ɗan adam, baya ga Amurka ƙasar Jamus ce ke kashe kuɗaɗe wajen taimakawa ɗan adam da zunzurutun kudi biliyan 2.52.

Baya ga taimakawa bil adama, Turkiyya na daukar matakan kare demokradiyya da kuma hakkokin bil'adama.

Turkiyya wacce ta kasance kan gaba a fannin taimakawa bil adama; ta na dauke da nauyin yan gudun hijira miliyan 3.5 a ƙasarta. Matakan da Turkiyya ke dauka domin tallafawa yan gudun hijira da sauran bil adama ya na da banbanci da na sauran ƙasashe.

Turkiyya na cigaba da mutunta ƴan adam musamman a halin yanzu da ƴan gudun hijira ke nutsewa a tekun Mediterranean da kuma ƙaruwar ƙyamar baƙi a nahiyar Turai da Amurka.

Misali, idan muka dubi al'amuran jam'iyyu masu tsattsaurar ra'ayi da kuma yadda Brotherhood party da Jam'iyyar Demokradiyyar Kiristawa a Jamus ke ƙara ɗaukar matakan kyamar yan gudun hijira. Nahiyar Turai dake da al'uma fiye da miliyan 550 na dauke da nauyin yan gudun hijira ƙasa da na ƙasar Turkiyya. Haka kuma a nahiyar Turai, kasancewar yadda jam'iyyu masu tsattsaurar ra'ayi ke ƙara bunƙasa, a inda a ko wacce ƙasar nahiyar, jam'iyya mai tsattsaurar ra'ayi take ta biyu ko ta uku ya sanya ƙara yaɗuwar lamurkan kyamar yan gudun hijira da baƙi a nahiyar.

Duk da a Turkiyya akwai yan gudun hijira sau uku fiye da na cikin nahiyar Turai ba'a samu rikicin ƴan gudun hijira a kasar ba. Haƙiƙa, Ingantaccen tsarin ƴan gudun hijira da harkokin tallafawa bil adama da Turkiyya keda shi sun ta'allaka ne akan kyekkyawar manufofin shugaba Recep Tayyip Erdoğan.Labarai masu alaka