Turkiyya na gaf da gudanar da zabe na tarihi

Sakamakon zaɓen Turkiyya zai ƙara darajar rawar da take takawa a yankunanta da ma duniya baki ɗaya. A daidai lokacin da Turkiyya ke ƙoƙarin samar da sauyi a yankin, ba zata yi wasa da yunkurinta na sauyin tsarin mulkin ƙasarta ba.

Turkiyya na gaf da gudanar da zabe na tarihi

Turkiyya ka yi samarwa Amurka da wasu ƙasashe dake da bukata a yankunan wata dama a yankin ta amfani da ɗan ƙarfin siyasa, tattalin arziki da sojan da take da shi. Ana dai hasashen lamurkan siyasar Turkiyya ciki da waje zasu ƙara ƙarfi bayan zaɓen da za'a gudanar ranar 24 ga watan Yuni.

Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Mal Yazar Can ACUN dake Cibiyar Siyasa da tattalin arziki wato SETA.

Kasancewar yadda lamurkan siyasar lraqi da Siriya suka kasa daidaita, akwai bukatar Turkiyya ta ƙara ɗaukar matakai a iyakokinta dake kudancin ƙasar. Turkiyya dai bata da niyyar kafa wata ƙasa a yankin kamar yadda ƙasashen yamma ke bukata. Akwai buƙatar a dauki kwararan matakai a gabas ta tsakiya da zaman lafiya ya ci tura. Haƙiƙa lamurkan siyasar Turkiyya zai ƙara gwaɓi bayan kammala zaɓen da zai tabbatar da sauya tsarin mulkin ƙasar. Zaɓen ƙasar Turkiyya da zai haifar da sabowar tsarin mulki a ƙasar zai kange dukkanin yunkurin canja taswirar lraqi da Siriya.

Akwai buƙatar Turkiyya ta ɗauki matakan kare tsaron ƙasar ta, musamman a yadda Amurka ke haɗa hurɗa da kungiyar YPG wacce ta kasance ɓarayin ƙungiyar PKK ce a Siriya da kuma yadda Rasha ke goyon bayan gwamnatin Asad da ma yadda lsra'ila ke ƙoƙarin katsa landan a harkokin yankin. Adai-dai lokacin da ƙasashen Turkiyya, Rasha da lran ke ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Siriya ƙarƙashin yarjejeniyar Astana ne Amurka ke haddaka da kungiyar YPG akan wata manufa daban. Albashin da Amurka ta baiwa mambobin YPG dubu 65 da kuma irin yadda Pentagon ta horar dasu bai kasance ba facce ƙalubale ga ƙasar Siriya da kuma tsaron kasar Turkiyya baki daya. A sanadiyar hakan ne Turkiyya ta tattauna da Amurka domin samar da mafita a yankin Membich dama sauran yankunan da kungiyar YPG ke mamaya baki daya.

Bayan kauda mafi yawan mambobin ƙungiyar DEASH da YPG an fara tunanin yadda za'a dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Siriya, za'a dai ɗauki ƴan lokuta kafin a fahimci halin da ƙasar Siriya za ta kasance nan gaba, kasancewar Turkiyya ƙasar da tafi ko wacce yawan makwabtaka da Siriya, ya zama wajibi a gareta da ta ɗauki matakai masu inganci a cikin waɗannan lokuta.

A ɗayan barayin kuma, kasancewar mambobin ƙungiyar ta'addar PKK a yankunan lraqi ya kasance wani ƙalubale ga Turkiyya, Akan hakan ne ƙasar Turkiyya ta fara daukar matakan soja a yankin. Da sannu a hankali za ta kauda kungiyar PKK da STK daga yankin daga bisani kuma ta ci gaba da daukar matakai a yankin Kandil. Turkiyta na daukar matakan kauda ta'addanci daga yankunan ta sama da kasa tare da  amfani da jiragen yaki marasa matuƙa kirar İHA da SİHA.

A ɗayan barayin kuma bayan kammala zaɓen ƙasar lraqi Turkiyya da gwamnatin lraqin sun yi wata haɗaka domin kauda kungiyar ta'addar PKK daga yankunan lraqin, wadanda suka mayar da tsaunukan Kandil da Sincar sansanonin su . Da zarar dai an kammala zaben kasar Turkiyya kasashen biyu dama hukumar arewacin lraqi za su ƙara ɗaukar matakan ƙalubalantar kungiyar PKK.

Canja tsarin mulkin da Turkiyya zata yi daga tsarin firaministan zuwa tsarin shugaban ƙasa zai warware matsalolin cikas ɗin da ake samu a lamurkan gwamnati, sabuwar tsarin zata sanya iya ɗaukar matakai cikin ƙanƙanen lokaci da kuma inganci, wannan dai lamarin da zai ƙara ƙarfafa ƙafafuwan Turkiyya a harkokin ta na yau da kullum.

Wannan sharhin Mal Yazar Can ACUN ne daga cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.

 

 


Tag: Turkiyya , Zabe

Labarai masu alaka