Matsalar da duniya ta gaza shawo kanta: 'Yan gudun hijira

Kamar kowanne mako, za mu duba sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara ya yi mana.

Matsalar da duniya ta gaza shawo kanta: 'Yan gudun hijira

Matsalolin Kasashen Duniya: 25

Masu karatu barkanmu dai tare da sakekasance wa a cikin sabon shirin Matsalolin kasashen Duniya. Ranar 22 ga watan Yuni rana ce da aka amince da ita a matsayin “ranar ‘yan gudun hijira ta duniya”. Rana ce ta tuna wa da mutanen da suke da matsalolin da aka kasa warware su, ko mun kalli matsalolin ma sai dai mu tattauna a kansu ba tare da daukar matakan da suka kamata ba don magance su.

A yanzu ana batun ‘yan gudun hijira miliyan 65 zuwa 70 ne. Idan aka kalli wannan adadi za a ga ya kafa kasa ta 20 mafi yawan mutane a duniya. Sannan kuma ana maganar mutane miliyan 400 da suka rasa matsugunansu.

Idan aka kalli wannan adadi za a ganshi a waje daya. Abu ne da ke da nauyi ga masu hankali da ba sa nuna damuwa, kuma abu ne da a zahiri ya ke da ciwo. Tare da hakan ana ganin yadda ake kashe wa, zalunta, cin fuska da muzantawa ga wannan adadi da ke zubar da hawaye. Ba za a iya tuna wa da irin wahalhalu da kuncin rayuwa da miliyoyin ‘yan gudun hijira da suka hada da jariria, yara, mata da maza manya suke ciki ba. Watakila a duk yankunan da aka gudu aka bari, to masu rayuwa a yankin sun fuskanci rushewa, rugujewa, hadiyewa da muzantuwa.

Shin waye zai so ya bar mahaifarsa da ta iyayensa da kakanni, tare da shiga jirgin ruwa ya jefa kansa cikin halaka tare da tafiya wajen da babu tsaro, wajen da bai ma san ina ne ba ko me zai je ya tarar? A duk yankunan da aka yi gudun hijira ana karkarewa da batun makomar mutanen da ma halin da suka bari a baya.

Kasashen da suka fi bayar da ‘yan gudun hijira su ne; Siriya, Afganistan, Sudan ta Kudu da Somaliya. Abu mafi ciwo shi ne, a shekarar 2010 Siriya ce kasar da ta fi kowacce karbar ‘yan gudun hijira amma a yau it ace ta fi kowacce bayarwa. Wadanda suke kasar ba su taba tunanin za su zama ‘yan gudun hijira ba, wannan ya kamata ya zama izina da masu kokarin korar ‘yan gudun hijira da hana su shiga kasashensu. Ga masu son gani ya kamata su duba tarihi domin cike ya ke da irin wadannan misalai. A yanzu kamar babu al’umar da ba ta taba zama ‘yar gudun hijira ba.

Kasar da ta fi kowacce bayar da ‘yan gudun hijira za mu ga ta fuskanci tsoma baki da mamayar yammacin duniya. matsalar ba wai ta samu bane saboda arangamar da kasashen duniya ba ne. Su kasashen da wadannan manyan kasashe suke arangama ne matsalar. A lokacin da manyan kasashe ke fafata wa su kuma ‘yan kasashen na zama ‘yan gudun hijira.

Babu kokwanto, tabbas ba wadannan manyan kasashe ne dalilin rikicin ba. Matsalolin cikin gida na kasashen, rashin shugabanci mai kyau, matsaolin siyasa, bukatun tattalin arziki, yunwa, fari, fatara da sauran matsaloli da dama ne suka janyo rikicin da ake yi. Su ne kuma suka janyo yawaitar gudun hijira.

Ana bukatar aiyuka sosai idan ana so a magance matsalar kwararar ‘yan gudun hijira. Amma a wasu lokutan matakai kanana ma na iya kawo karshen matsalar. A Afirka kudin gina rijiyar birtsatse ba shi da yawa. Wannan kadai zai iya hana jama’ar kauyen gudun hijira gaba daya. Irin wadannan matakai watakila ba za su kawo karshen matsalolin ba amma akalla za su rage radadin da ake fuskanta tare da tabbatar da niyyarmu. Hakan zai zama kamar tururuwar da ta dibi ruwa don kashe wutar da za a kona Annabi Ibrahim Alaihissalam. Ko da a ce irin wadannan matsaloli ba za su amfanar da mu ba, amma za su iya sauya rayuwar mutanen da ke amfana da su. Kamar kokarin mutumin da dibi kifaye da suka gangaro gabar tekuya ce zai mayar da su da hannu, zai dai dibi dan abin da zai iya ne kawai amma ya fi babu. Ama kuma duk wanda ya mayar ya kubutar da rayuwarsa. Abin da ke kare martabar dan adam shi ne abin da wasu suka yi masa ba wai arzikinsa ba.

Shin zai wadatar idan muka tsaya ga gano matsaloli ‘yan gudun hijira, yin bakin ciki ba tare da yunkurin magance su ba? Shin ba za mu dora alhaki ciwon da ake ji ba kan wadanda suka janyo shi?

Tabbas a a. Za mu soki tare da nuna adawa da dukkan shugabanci mara kangado da ya bar al’umarsa cikin munin hali, tare da jefa makomarsu cikin mawuyacin yanayi. Dole ne mu bayyana yadda ‘yan mulkin mallaka suke jafa mutane da kasashensu cikin mummunan hali da kuncin rayuwa.

Tare da dukkan wannan, dole ne mu yaba wa kasashen da suka yi kokari a duniya wajen amfani da hankali da ka’idoji ba wai da siyasa zalla ba. Duk da cewa ba ita ce kasar da ta fi kowacce arziki a duniya ba, amma Turkiyya ta fi kowacce kasa ta duniya karbar ‘yan gudun hijirar Siriya. Bayan ta sai Jordan da Labanan. Adadin da wadannan  kasashe suka dauka na ‘yan gudun hijira ya ninninka na sauran kasashen duniya. Adadin mutanen da garin Kilis na Turkiyya ya dauka na ‘yan gudun hijira ya fi adadin yawan wadanda wasu kasashen Yamma suka dauka. Tun daga farkon rikicin zuwa yau an haifi ‘yan kasar Siriya sama da dubu 300 a Turkiyya. Kuma wadannan kasashe ba wani bangare ba ne na rikicin Siriya.

A gefe guda kuma, Manyan Kasashen Duniya, sun zama wani bangare na rikicin Siriya. Masu nuna damuwa ga Siriya da yawansu suna yi ne don samun damar sayar da makamai tare da nuna kawunansu.

Ya kamata Kasashen Duniya su magance wannan abin takaici da ake yi. Dole ne su yi amfani da dan adam, tunani mai kyau, Addini, Siyasa da ra’ayin rayuwa wajen kawo karshen wannan matsala.

Dole ne a sake daukar wasu matakai don kawo gyara. Wannan ma ba wai manyan kasashen duniya ne matsalar ba, wannan aiki ya fada kan kungiyoyin fararen hula ne. A lokacin da manyan kasashe da aiyukansu suka zama musabbabin gudun hijira, amma warware matsalolin kuma na kan kungiyoyin farar hula na kasa ko yankuna.dole kungiyoyin kasa da kasa su hada kai wajen kawo karshen wannan matsalar. Dole su hada rahotanni, nazari tare da sanar da sauran kasashen duniya. Asali wannan aiki ba na kungiyoyin farar hula ba ne kawai, aiki ne da ya ke kan kowannen mu. Kar mu manta cewa, matsalar dan adam da mu magance ba ba wai za ta sama mu zama marasa kangado ba ne kawai, duk matsalar dan adama da ba mu warware ba to za ta dawo kanmu wata rana tare da yin tafiyar ruwa da mu.

Sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara ya yi mana.

 Labarai masu alaka