Me ya sa ba a kalaman rarrabuwar kai a lokacin zaben Turkiyya?

Kamar kowanne mako muna dauke da Sharhin Ferfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

Me ya sa ba a kalaman rarrabuwar kai a lokacin zaben Turkiyya?

Matsalolin Kasashen Duniya: 24

Masu karatu barkanmu dai tare da sake kasancewa a cikin sabon shirin Matsalolin Kasashen Duniya. Nan da wani dan lokaci za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a Turkiyya. ‘yan takara da jam’iyyun siyasa na ci gaba da gangamin neman kuri’ar jama’ar kasa. Idan aka kalli tarihi ta fuskar wannan ne karo na farko da Turkiyya za ta yi zaben Shugaban Kasa za a ga cewa, akwai wani saukin ra’ayi da ba a taba ganin irin sa ba. Kuma babu kalamai masu zafi na an raba kan al’uma a lokacin da ‘yan takara suke bayanai a wuraren kamfe.

Domin samun %50+1 sai an yi siyasar hada kai da kulla yarjejeniya

Idan aka kalli zabukan baya za a ga cewa, da yawan kuri’u kaso 20 cikin dari ana iya hawa karagar mulki. Jamiyyar AKP ta zabi tsarin da ita kanta yana da wahala gare tainda ta kawo ka’idar sai mutum ya samu kaso %50+1 na kuri’un da aka jefa sannan zai zama shugaba. Daga yanzu abinda jam’iyyu suke da shi ba zai ishe su ba. ‘yan takara ya zama dole sai sun tuntubi bangarorin al’uma daban-daban domin samun adadin kuri’ar da suke so. Hakan ya sanya sai sun je wajen masu jefa kuri’a tare da jan ra’ayinsu. Tsarin sai an samu %50+1ya sanya jam’iyyun barin tsohon tsari tare da koma wa kan sabo. Saboda haka babu bukatar ‘yan takara da jam’iyyu su yi kalamai munana domin suna bukatar fadada zuwa ga masu jefa kuri’a da dama.

Idan aka yi tunani game da wahalar yankuna kan gudanarwa a Turkiyya, yadda ya zamar wa ‘yan takara wajibi su hada kai tare da kulla yarjejeniya abu ne mai kyau.

Yiwuwar kai wa ga zagaye na 2

Duk da yadda kuri’un jin ra’ayin jama’a suke nuna za a kammala zaben a zagayen farko, amma ‘yan adawa na ta kokarin ganin sai an je ga zagaye na biyu. Tunanin akwai yiwuwar a kai ga zagaye na 2 ya sanya ‘yan takara kin yin kalamai masu tsauri. Musamman ‘yan adawa da suka san ba za su samu %50+1 daga jama’arsu ba, hakan ya sanya suke karkata ga sauran jam’iyyu da suka hada da AKP don samun wasu kuri’u. Shi ya sa ‘yan takarar suke ta kalamai na nuna rungumar jama’a baki daya. Ba sa nuna cewa, ga nasu ko jam’iyyarsu kawai ita ce.  Babu jam’iyyar da ke munana kalamai saboda akwai yiwuwar ta zama ita ce za ta kai ga zagaye na 2. Za kuma a ga tasirin da zuwa zagaye na biyun zai kawo. Idan aka samu hakan to jam’iyyu za su shiga yarjejeniya ta daban. Za su zo su bukaci kuri’un ‘yan sauran jam’iyyu shi ya sa ba za su tsaurara kalamai ba.

Masu jefa kuri’a su fitar da dan takara kai tsaya

A zabukan Shugaban Kasa da suka gabata, kawai kungiyoyin majalisa na jam’iyyu ko wani adadi na ‘yan majlisa ne suka fitar da dan takara. Asali wannan yanayi yana da hatsari game da akwatunan zabe ta yadda ba ra’ayi masu jefa kuri’a ba ne. Hakan wani nakasu ne na demokradiyya da ‘yanci. Sabon tsarin ya tafiyar da wannan nakasu. Kowa zai iya zama dan takarar shugaban aksa idan ya samu saka hannun mutum dubu 100. Wannan tsari ya kawo dama ga kananan jam’iyyu da kungiyoi tsiraru. Da ba a bayar da wannan dama ba da jam’iyyu ko kungiyoyin sun nuna tsauri. Amma saboda damar sun zama za su iya tsayar da dan takara. Idan mutum bai samu sanya hannun mutum dubu 100 to ba zai dora laifin kan tsarin kawai ba.

Kafa hadin kai tun kafin zabe

A zabukan baya ba a yarda jam’iyyu su hada kai waje guda ba a lokacin zabe. A wannan zaben saboda damar hadin kai da aka bayar dukkan jam’iyyun suna bangare hadin kan Jamhuriya ko na Kasa. Yadda jam’iyyun siyasa suka shiga zabe ta hanyar hadin kai ya rage wasu rikice-rikice guda biyu. A baya ana hada kai ne bayan zabe ,dan an zo kafa gwamnati. A lokacin zabe kowa na kokarin kai bantensa ne. A yanzu da aka bayar da damar hada kai kafin zabe ya sanya kawar da abubuwan da aka fada a sama tare da sassauta kalaman da ‘yan takara suke yi a lokacin yakin neman zabe. Yin hadin kai kafin zabe na bayar da dama wajen gabatar wa da masu jefa kuri’a da za su yanke hukuncin amincewa ko kuma a a.

Agefe guda yadda hadin kai ke bayar da damar shiga zabe ba tare da batun samun kaso 10 na kuri’u ba, ya sanya kananan jam’iyyu ma za su iya shiga majalisa. Idan aka samu karin jam’iyyun siyasa a majalisa yana rage rikicin siyasa a kasa.

Siyasar nuna wariya ba za ta samu wajen zama ba kwata-kwata

A lokacin yakin neman zabe babu batun nuna wariya ko bambanci musamman ma daga bangaren ‘yan hagu da suke yawan yn batun Mai ci baya-Mai ci gaba, Mai Addini da Mara Addini, Zamani, Ra’ayin Ataturk, da dai sauran kalamai na nuna bambancin ra’ayi ko akida. Ba daidai ba ne a ce wannan abu ya yaga jam’iyyu gaba daya kuma a lokaci guda ba. Abinda ya sauya wannan kalami shi ne sauyawar tsarin zaben. Yadda kowa ya san jama’arsa ba za su ba shi kaso %50+1 ba, hakan ya sanya jam’iyyun sake nazarin manufofin da suke akai gwamman shekaru. Idan ana so a hau mulki ba ta hanyar siyasar nuna wariya ba ne, bukatar samun goyon bayan jama’a mafi rinjaye ne. Yadda jam’iyyu ke kulla alaka da sadarwa ga al’umu daban-daban ci gaba ne ga Turkiyya.

Nuna wariya ga reshen ‘yan ta’adda

Wani da ya sake jan hankali a lokacin yakin neman zabe shi ne yadda jam’iyyar HDP da ta ki nesanta kanta da ‘yan ta’adda babu wanda ya kulla kawance da ita. Wannan taron dangi na da ma’ana da alfanu ga ka’idojin demokradiyya. A ce jam’iyyar siyasa na tsaya wa takara da neman kuri’ar jama’a, bayan an samu nasara kuma sai su koma tsaunuka wajen ‘yan ta’adda tare da karbar umarni daga wajen ‘yan ta’addar da ba a zabe su ba.

Daduwar son al’uma bakuwa

A lokacin yakin neman zabe da shirya shi, yadda ake nuna bukatar neman kuri’un al’umu daban-daban na nuna daduwar sn wasu al’umun daban a tsakanin jama’a. Musamman jam’iyyun adawa ba suna maganar me za su samar ba nekuma ta yaya za su samar da shi, a a suna ta batu ne a kan me za su rarraba ga jama’a. Wannan kuma ya samuu ne saboda kasar ta zama ba ta dala budu 2 a a ta dala dubu 10. Da yadda ba ta bukatar cent 80. Tare da hakan shugabannin ne za su dauki alakin duk wani abu da aka kashe ko haraji da suka afkuwa wajen nuna bukatar jama’a. Haraji da ya ke karuwa yana durkusar da kasuwa fararen hula tare da rage yawan kayan da ake samarwa. Idan za a yi wa kowa alkawarin koma kyauta to a karshe za a wayi gari ba a samar da komai ba. Ma’ana hakan daidai ya ke da babu.

Sabuwar siyasa: Ba ta mai sabani ba ce, gudu ce zuwa ga abu mai yiwuwa

A yankin da Turkiyya akwai hadurra da ke gabanta sosai, a siyasar cikin gida kuma ba rabuwar kai ba hadin kai, ba rarraba al’uma ba hada su waje guda, ba siyasar wane ne kai ba ko ta karamar kabila, ta aminta da manufofi masu kyau na masu rinjaye a cikin al’uma, darajar rayuwa na da muhimmanci game da wanzuwar kasa. Tsarin shugaban kasa wajen mulki na tabbatar da wannan abu tun daga yanzu. A kokarin jam’iyyu na samun kuri’u daga kowanne bangare sun zama masu neman abinda zai yiwu ba wai nuna wariya da bambanci ba.

Siyasa da ma aiki ce kan abinda zai yiwu.

Sharhin Ferfesa Kudret Bulbul Shugaban tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’an Yildirim beyazit da ke Ankara.

 Labarai masu alaka