TURKIYYA TA SHIGA WATAN RAMADHAN TARE DA AIYUKAN WARWARE RIKICE-RIKICE

A daidai lokacinda duniya ta zama wajen da aka kasa juyawa, ake fama da yakin basasa da yake-yake, aka shiga zamani na rikici, watan Ramadhan na gafara da Rahma ya riske mu tare da samun labarin zubar da jinin al’umar gaza da suka yi Shahada.

TURKIYYA TA SHIGA WATAN RAMADHAN TARE DA AIYUKAN WARWARE RIKICE-RIKICE

A lokacin da Isra’ila ke bikin ranar kafa kasarta, masu aiyuka na ci gaba a lokacinda Falasdinawa dubu 750 suka zama ‘yan gudun hijira a cikin kasarsu. Ku duba wannan abun takaici.

Matsayin Kudus

A tsawon lokaci da Addinai Ibrahimi suka wanzu a Kudus ba a ba wa garin wani matsayi na musamman ba. Akwai dalilan da ya sa babu wata kasa a duniya da ta ce Kudus Babban Birnin Wata Kasa kuma babu wadda ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa Kudus. A saboda haka doka ta 181 ta Majalisar Dinkin Duniya da aka samar a 1947 an bayyana Kudus a matsayin birni na kasa da kasa. Bayan kafa Isra’ila a 1948 sai a shekarar 1967 ta mamaye yammacin Kudus ta hanyar yaki cikin kwanaki 6 inda daga baya kuma ta mamayi Gabashin Kudus. Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi abinda ya kamata wajen samar da doka ta 242 don samar da adalci a Gabas ta Tsakiya inda ya bukaci Isra’ila da ta janye daga inda ta mamaye. Amma tun wannan lokaci Isra’İla ta kafa majalisarta da ginin m’aikatunta a Kudus. A shekarar 1980 Isra’ila ta yi doka kan kudus na ya zama Babban Birninta amma Majal,sar Dinkin Duniya ta yi doka ta 478 tare d asukar wannan mataki, kuma ta nemi duk wata kasa da t mayar da ofishin jakadancinta zuwa Tel Aviv. Amurka ba ta halarci taron jefa kuri’a kan kudirin ba kuma ba ta yi amfani da karfin ikonta wajen hana amfani da shi ba saboda matsayin na mamban didndidn a Kwamitin Tsaro. Tun daga sannan kasashen Bolibiya, Jamhuriyar Dominic, Guatemala, Kolmbiya, Panama, Uraguay, Equador, Chile da Venezuela suka fara dauke ofisoshin jakadancinsu zuwa Tel Aviv. A shekarar 2006 El Salvado da Costa Rica suka dauke ofisoshin jakadancinsu daga Kudus inda daga sannan babu ko daya da ya yi saura a birnin.  

Me Amurka ke aikatawa?

A  shekarar 1995majalisar dokokin Amurka ta samar da wata doka wadda ta saba wa dokar Kwamitin Tsaro na MDD mai lamba 478 inda suka ce za su mayar da ofishin jakadaninsu zuwa Kudus daga Tel Aviv. Dokar ta tanadi cewa, zuwa 1999 ne za a kammala mayar da ofsihn zuwa Kudus. Kuma duk shugabannin Amurka da suka wuce sun hango matsalar da ahakan zai janyo wanda ya sanya suke ta dage lokacin.

A ranar 6 ga watan Disamba, 2017 ne aka cika shekaru 100 da bayanan Balfour suka ayyana kasar daular Usmaniyya a matsayin ta Yahudawa. Kuma shugaban Amurka na 45 Donald Trump ya bayyana mayar da ofishin jakadancincu zuwa Kudus daga Tel Aviv. Wannan sanarwar ta zama wata babbar matsala ta tarihi da ta kara lalata aiyukan samar da zaman lafiya a Gabas ta tsakiya da ake yi. Wannan yunkuri na Trump ba karain abu nei wani bangare na mamayar kasa da kasa.

Amurka ta rufe ido tare da take dokokn kasa da kasa duk da kasashen duniya sun ce a a amma ita ta ce eh dk da sanin wannan abu zi janyo karuwar arangama amma sai da ta mayar da ofishin zuwa Kudus. Wannan abu ta yi shi ne don tabbatar da goyon bayanta ga Isra’ila.

Yadda ake saka wa Falasdinawa takunkumi, rufe musu hanyo to wannan hukunci ma haka ya ke. Duk da martanin kasashen duniya amma Amurka ba ta fasa wannan danyen aiki ba. Falasdinawa sun nuna bacin ranzu tare da harzuka bisa wannan matakida Amurka ta dauka. Sannan kuma an yi amfani da karfi da ya wuce kima wajen zaluntar farar hula da suka tashi yin zanga-zanga. Duniya na kallo, a kan idon kafafan yada labarai ‘yan sandan Isra’ila suke karkashe Falasdinawa inda suke yin Shahada. Sun kuma jikkata wasu dubunnai. Shekaru 70 kenan da ranar Nakba wadda ta ke nufin babbar musiba da ta samu Falasdinawa suka rasa matsugunansu tare da zama ‘Yan gudun hijira marasa kasa a cikin kasarsu.

Türkiyya mai dauke da ruwan kashe gobarar Gabas ta Tsakiya

A ranar 18 ga watan Mayu ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gayyaci kasashe mambobin Kungiyar Hadin Kan Musulmi ta Duniya zuwa Istanbul don gudanar da taro kan Kudus. Erdoğan shi ne shugaban Kungiyar a halin yanzu.wannan taro na da muhimmanci duba da rawar da ya taimaka wajen mayar da martanin “Dakata” kan wannan aika-aika ta Trump. Duk duniya ta dinga magana akan taron saboda ya yi nasara kan abubuwanda kungiyoyin kasashen duniya da dama suka kasa yi. Ta hanyar yunkuri da tausayin Turkiyya an tabbatar da matsayin Kudus a yadda ya ke na ba mallakar wata kasa ba.  

A yayin Turkiyya ta bayyana cew, wannan matsala na cutar da Isra’ila, wannan abu ba zai kawo karahsne matsalar Falasdinawa ba da MDD ta kasa warwarewa tun sanda aka kafa ta, haka kuma za ta sake rurar wutar rikicin ne kawai tare da mayar da yankin cikin wuta. Turkiyya ce kasa ta farko da ta fara nuna dole a kawo karshen rikici da yakin da ake yi a yankin. Amma duk da haka abin takaici kasashen da abin ya shafa sun ki su yi wani katabus.

A lokacinda aka aika jirgin ruwan Mavi Marmara don taimaka wa wadanda aka zalunta, an kashe mutane ‘Yan ba ruwana da ba sa dauke da makamai. Domin rage wutar rikicin tare da sassauta zalunc,n da ake wa Falasdinawa Turkiyya ta nemi Isra’ila da ta nemi afuwa tare da biyan diyyar rayukan da ta kashe da jikkatawa. Amma an y amfani da farfaganda wajen hana tabbatar da wannan yunkuri. An kirkiri krya indz ake cewa, Hukumar TIKA da ta raini matasa dubu 400 wai na taimaka wa ‘Yan ta’adda ne. Taje yankin ne don bayar da gudunmowar lafiya ba wai wani abu ba.

Idan aka yitunani mai kyau, za a ga yadda taimakon Turkiyya ya sasauto da rikicin tare da rage hadurran da ake fuskanta. Duk da haka Turkiyya ta ci gaba da aiyukna neman tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A wannan wata na Ramadhan, an bayar da kayan taimako na lafiya ga mutanen da aka jikkata sannan kowacce rana ana ciyar da iyalai dubu 1000 inda sukakai mutum dubu 200 a kowacce rana suna samun abincin bude baki mai zafi. Ana kai marasa lafiya asibiti da gidajensu. Aiyukan da ake na taimako da samar da zaman lafiya za su taimaka wajen dadawa Falasdinawa rayukansu.

Turkiyya na bayar da goyon baya wajen a tabatar da adalci a samu warware rikicin ta hanyar daukar bukatun kasashen 2. Kuma wannan abu da ya hada da neman halarcin kowacce kasa zai taşimakawa Isra’ila. Ya zama dole Isra’ila ta daina kashe flasdinawa, kai musu hari da bam, zartar musu da hukuncin kisa ba tare da shari’a ba, gina katanta a yankunansu inda maimakon haka kamata ya yi ta ji tausayi, jin kai da kare Falasdinawa.  

Turkiyya mai hankoron ganin kawo karshen rikicin

Turkiyya da ta ke da al’adu na rahma da adalci, ta ke da tarihi na aiyukan diplomasiyya ta kasance tana kasancewa tare da wanda aka zalunta a koyaushe ba tare da kallon Addini, Yare ko Launin Fatarsa ba. Akwai misalai da dama da zza a iya gani na wannan ikirari a cikin tarihi. A shekarar 1892 Yahudawa dubu 200 da suka fuskanci zalunci a Spaniya sun nemi mafaka a Daular usmaniyya inda sula sami’yan ci da farinciki a daular. A daular Usmaniyya Yahudawa sun rike mukamai da dama. A zamanin Jamhuriya ma za a iya ganin abu makamancin haka. Alokacin yakin duniya na 2 Turkiyya ta yiiya kokarinta na kare Yahudawa daga zaluncin Nazi. Jakadan Turkiyya a Marcelle Necdet Kent ya buga fasfo tare da kubutar da Yahudawan da ake shirin kora daga Faransa zuwa Jamus wanda wannan abu da ya yi na iya jefa rayuwarsa cikin hatsari. Haka ma Jakdan Turkiyya da ke Rodos Selahattin Ulkumen ya ki mikawa Janaral din Jamus wasu Turkawa-Yahudawa da ke zaune a sansanin Rodos wadanda ake kokarin mayar da su Jamus. Idan aka kalli taihi to za a fi yarda da irin kokarin da Turkiyya ke yi a yau.

A dukkan yankunan da Turkiyya ke wa kallon wani bangare nata ya kamata a girmama irin kokarin da ta ke na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kasar da ta ke dauke da gadon Daular Usmaniyya wadda ta yi jagoranci na shekaru sama da 400 tsakann mutane mabiyar Addinai daban-daban da kabilu da launifa mabambanta, to tabbas babu kokwanto da gaske ta ke wajen aiyukan da ta ke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunanta. Zaku ata taka muhimmiyar rawa a wajen wannan aikin.  

Manufar Turkiyya ba shi ne ta mamay,i wata kasa tare da yi mata mulkin mallaka ba ta hanyar kwashe dukiyarta, abinda ta ke son yi shi ne, mutanen da suke rayuwa a wajen kasarta su sami walwala da jindadi su ma a tayuwarsu ta yau da kullum. A saboda haka Turkiyya ba tana da mutane miliyan 80 ba ne, a a tana da biliyan 7.5 ne wato dukkan al’umar duniya ta ke kokarin samawa salama. An ga irin kokari da gaskitya ta Turkiyya a Myammar da Bangaladash ‘ watannin da suka gabata. Turkiyya ta rungumi tare da kai dauki ga Muaulman Arakan da suka nemi mafaka a Banagaladash.saboda Shugaba Erdoğan tun bayan fara rikicin ya dinga jan hankalin duniya tare da ganawa da shugabanni ta hanyar diplomasiyya.hukumar TIKA ta aike da kayan taimako ga dubunnan Musulman Arakan da suke neman mafaka a Bangaladash wadanda suke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira.waye zai ce Turkiyya ta tafi har sama da kilomita dubu 5,500 don kai taimako don amfanin kanta? Manufar Turkiyya ba ta wuce kokarin da ake yi na magance rikicin da ake yankunan da aka mayar da su yanayin da ba za a iya jogarantar su ba.  

Alakar Turkiyya-Isra’ila

Jamhuriyar Turkiyya na kallon alakar diplomasiyyarta da Isra’ila a matsayin wani yunkuri da zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu. İdan aka yi tunani kan irin yaki da Isra’ila ke yi da kasashen yankinta, to wannan alaka tana tamaka wa wajen hana barin Isra’İla ita kadai.

A duk lokacin d aka yai rikici tsakanin Falasdinawa da Isra’ila to alakar Turkiyya da Isra’ila na ja baya. Tsaiwar daka da Turkiyya ke nuna wa ba ya yi wa gwamnatin Isra’ila dadi wanda rikicin diplomasiyya ke barkewa tsakanin kasashen 2. Bayan rikicin Gaza na karshe d aka fuskanta, jakadun kasashen sun koma gida na wani dan loakci, hankulan mutane sun fara tambayar ko alakar dşiplomasiyyar za ta sakwarkwace ko kuwa a a. Komawar jakadun zuwa kasashensu na wani lokaci abu ne maikyau amma kuma rushewar alakar dioplomasiyyar za ta zama kamar wani takunkumi ne ga Falasdinawa da ake cuta da zalunta. Rikicin watanni 6 da aka yi bayan harin Mavi Marmara, sake aika jakadu zuwa kasashen ya sake rage wutar rikicin inda hakan ya sake saukaka wa Turkiyya aiyykan da take na bayar da taimako ga Falasdinawa. A saboda haka ana mamayar Kudus, ana rufe hanyoy da gina katanga a Zirin Gaza sannan kuma Jammacin Gabar Kogin Jordan na krkashin mamaya. Kuma dukkan hanyoyin da ke kaimwa ga Falasdinawa na karkashin ikon Isra’ila. A wannan gaba dole ne a nisanci azarbabi tare da amfani da hankali wajen guje wa abubuwan da za su sake ruwa wutar rikicin. Dole ne hukumomin su taka rawa wajen tabbatar da wannan abu. Hukumar TIKA ya kamata ta dinga tuntubar ofishnmu kan aiyukanta a wadannan yankuna. A yau gwamnatin Isra’ila ko ma ba ta taba yi ba to ya zama dole ta bude kunnuwanta tare da sauraren kasashen duniya sannan ta dakatar da zaluncin da ta ke yi wa Falasdina. Mutane da suka fi kowa shiga tasku da gudun hijira a tarihi, bai kamata irin abun da suka fuskanta a baya ba a yanzu su zama suna jefa wasu a cikinsa. A gefe guda ana ganin yadda wata kasa a yankin ta ki daukar aiyukan shiga tsakani don kawo karshen wannanj rikici. Kamar yadda ya ke a baya dole Birnin Kudus ya zama mutane mabiya Addinai daban-daban suna rayuwa a cikinsa tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Babu shakku a duk lokacin da wata al’uma ta samu ‘Yanci da tsaro wajen gudanar da al’amuranta to za a samu salama da zaman lafiya a kowacce unguwa da ake kasuwanci. A yankunan da TIKA ta ke zuwa tana karfafa irin tushen da aka dora yankunan a kaitana kokarin samar da zaman lafiya da walwala, tana sake gina duk wasu wurare da aka lalata. Wannan shi ne aiyukanta ba wani wani abu daban ba.Labarai masu alaka