Lamurkan da suka sanya tangarda tsakanin Turkiyya da Amurka

A sanadiyar faruwar waɗansu lamurka a cikin ƴan shekarun nan tsakanin Turkiyya da Amurka sun sanya yin tsamin dangantakar ƙasashen biyu.

Lamurkan da suka sanya tangarda tsakanin Turkiyya da Amurka

A sanadiyar faruwar waɗansu lamurka a cikin ƴan shekarun nan tsakanin Turkiyya da Amurka sun sanya yin tsamin dangantakar ƙasashen biyu. Musamman yadda Amurka ta ƙi miƙawa Turkiyya shugaban ƙungiyar ta'addar FETO, Fethullah Gulen da suka yi yunkurin juyin mulki da kuma yadda Amurkan ke haɗaka da kungiyar YPG a Siriya wacce wata ɓarayin kungiyar ta'addar PKK a Turkiyya ce.

Adai-dai lokacin da dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara raguwa ne Turkiyya ta ɗaura ɗamarar yaƙi da ta'addanci inda ta ƙaddamar da hare-haren Firat Kalkanı da na reshen zaitun. Bisa ga sharuɗar yarjejeniyar Astana kuma, rundunar sojan Turkiyya sun samar da yankunan lumana har 12 a ldlib, Turkiyya dai ta yi iya kokarinta wajen kauda ƴan ta'addar PYG a lokacin hare-haren lamarin da ya inganta lamurkan tsaron yankin Membich.

Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Malam Yazar Can ACUN dake Cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA 

Yankin Menbiç ya kasance ƙarƙashin ikon sojojin Siriya masu zaman kansu a farkon fara juyin juhani a Siriya. A shekarar 2014 kungiyar DAESH ta mamayi yankin bayan haka a shekarar 2016 ne kungiyar YPG ƙarƙashin jagorancin Amurka da sojojin Siriya suka fara kai farmaki a yankin. A sanadiyar korafi da ƙalubalantar da Turkiyya ta yi wa wannan lamarin ya sanya Amurka yin alƙawarin za ta janye mambobin YPG daga yankin Afrin bayan ta kauda kungiyar DEASH tare da miƙa ikon yankin ga larabawa. Duk da wannan alkawarin da Amurkan ta yi har ila yau mambobin YPG basu ƙaurace daga yankin ba, suna ma amfani da kwamitin sojojin  da Amurka ta kafa a Membich a matsayar ja gaban su, duk da kasancewar kwamitin sojojin ƙasar masu zaman kansu Jamil Mazlum da lsmaila Derik waɗanda kungiyar ta'addar PKK ta tura yankin  Membich  ɗin ke jagorantar ta. Bugu da ƙari kamar yadda kafafen yaɗa labaran yankin ke rawaito wa, kwamitin na ƙoƙarin yaɗa akidar kungiyar ta’addar PKK-YPG ga daliban makarantun dake yankin.

Babban dalilin da yasa Turkiyya ke iya kokarinta a yankin Membich shi ne ganin yadda al’umar yankin suka tsawalu da kama karyar da kungiyar YPG ke yi. Hakika, dubban mutanen da suka yi hijira daga yankin Membich domin tserewa daga zaluncin kungiyar YPG sun nemi mafaka ne a yankin da aka kubutar yayin hare-haren Fırat Kalkanı. Bugu da kari, kabilu da sauran mazauna yankin sun gudanar da zanga-zanga domin kalubalantar yadda matasan kungiyar ta’addar YPG ke muzguna musa da sanyasu daukar makamai don döle. Kungiyar Al-Qiam wacce aka kafa a Membich ta fara aiyukan gaske a yankin a yayin da ta fara kashe wasu mamabobin kungiyar YPG.

Bayan kammala hare-haren reshen zaitun sanarwar da Turkiyya ta fitar dake nuna cewa za ta iya kaddamar da hare-hare a yankin Membich ya sanya shugabanin kasashen biya fara tattaunawa akan lamurkan. Da farko dai a lokacin da tsohon ministan harkokain wajen Amurka Rex Tillerson ya ziyarci Turkiyya an kulla hadaka tsakanin Turkiyya da Amurka domin samar da hanyar warware matsalolin yankin Membich kai tsaye, duk da an samu dan tsaiko bayan canja Rex Tillerson sabon ministan harkokain wajen Amurka Mike Pompeo ya dora daga inda Tillerson ya tsaya. Akan wannan hadakar Turkiyya da Amurka sun aminta akan mataki uku. Da farko dai shi ne kauda mambobin kungiyar YPG daga yankin Membich, kulla hadakar bai daya tsakanin Turkiyya da Amurka domin kula da Membich da kuma mika ikon Membich ga mazauna yankin.

Hadakar da kasashen biyu suka kulla ya sanya rage kace na ce tsakanin kasashen biyu wadanda dukkansu mambobin kungiyar NATO ne, duk da haka dangantakar kasashen biyu nada kalubale a wasu wurare, idan har ba’a fara anfani da ka’idojin da kasashen biyu suka kulla ba, idan har ba’a janye mamabobin YPG daga Membich ba- hakika ko shakka babu dangantakar kasashen biyu ka iya ci gaba da tsami. Tabbas ya kamata kasashen biyu su warware matsalar hurda da kungiyar PKK/YPG. Duk da Amurka ta bayyana cewar kwamitin sojojin da ta kulla a Membich masu zaman kansu ta kasance kwamitin da wasu mamabobin kungiya ke jagoranta. Wani matsalar dake tsakanin kasashen biyu kuma ita ce kasancewar mamabobin YPG a Afrin. Turkiyya dai na bukatar a dauki matakin kauda dukkan mambobin kungiyar ta’addar YPG daga yankin Membich, sabili da, kasancewar mambobin YPG a Membich babban kalubalen tsaro ne ga Turkiyya da ma yankin baki daya. Ita kuwa Amurka ba ta bukatar a dauki irin matakin da aka dauka a Membich a yankin Afrin musamman a gabashin Siriya  mai arzikin man fetur da kungiyar ta’addar YPG ke iko.

Duk da ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu da takawansa na Amurka Mike Pompeo sun aminta akan lamurkan Membich, dangantakar kasashen biyu zai ta’alaka ne akan aiyanar da yarjejeniyoyin Membich din da aka aminta akansu.

Wannan sharhin Mal. Yazar Can Acun ne masani a hukumar nazarin siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.Labarai masu alaka