Tun kafin a fara aiki da Tsarin Shugaban Kasa ake son watsi da shi?

Sharhin da Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana wanda shi ne Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

Tun kafin a fara aiki da Tsarin Shugaban Kasa ake son watsi da shi?

Matsalolin Kasashen Duniya: 23

Masu karatu barkanmu dai tare da kasance wa a cikin shirin Matsalolin Kasashen Duniya. A ranar 24 ga watan Yuni Turkiyya za ta gudanar da babban zabe karo na 32 kuma na farko na Tsarin Amfani da Shugaban Kasa wajen mulki. Jam’iyyar AKP, Kawancen Jamhuriya na bayyana alkawaransu kan yadda za a magance mtsalolin Turkiyya idan aka yi nasarar kom wa tsarin amfani da shugaban kasa wanda jama’a suka jefa kuri’ar amincewa, amma bangaren hadin kasa kuma yana cewa, idan ya yi nasara za a koma amfani da tsarin shugabanci daga majalisar dokoki. Har sun fara tattaunawa kan idan har suka yi nasara to za su koma amfani da tsarin na majalisa cikin gaggawa.

Ko ta yaya jam’yyun hamayya za su nuna adawa to su yi hakan, shi tsarin amfani da shugaban kasa jama’ar Turkiyya ne suka jefa kuri’a tare da amince wa da shi. A ranar 24 ga watan Yuni tsarin zai fara amfani. Ba abu ne mai yiwuwa ba da hankali zai amince yadda wadannan ‘yan hamayya ba su gwada amfani da sabon tsarin ba, ba su ga ko zai warware matsalolin Turkiyya ko kuma ba zai yi ba amma gaba gadi sai suke adawa da watsi da shi. Sama da hakan ma, sabon tsarin da suke so su dawo da shi tsari ne da tsawon shekaru 140 ya janyo wa Turkiyya matsaloli da dama.

Tabbas babu shakku za a iya kallo da tattauna wa kan kasashen da ake amfani da tsarin shugabanci da majalisa ta hanya mai kyau. Amma idan aka kalli Turkiyya ta fuskar tarihi za a ga yadda tsarin ya janyo wa Turkiyya matsaloli, ya sanya aka kasa gudanar da gwamnati da ma yadda aka dinga tsoma bai kan gwamnati daga Kasashen waje. (Game da wannan batu za a iya samun bayani kan rubutun da na yi a baya na dalilan daya sa ake bukatar tsarin shugaban kasa da abu wan da akea gano da wadanda ake jiran samu).

An sani sosai yadda kundin tsarin mulki na 1961 ya sanya sojoji da alkalai suka zama matsala ga ‘yan majalisu da ke wakiltar al’uma ta yadda majalisa ba ta da iko a kansu. Har yanzu radadin yadda aka zartar da hukuncn kisa kan Firaminista da ministoci bai wuce ba, ba a manta da yadda ake wa majalisa kawanya ba wajen zaben shugaban kasa a baya ba.

Haka zalika ba a manta da tsarin zabe, katsalandan daga kasashen waje da rikicin siyasa mummuna da aka samu ba, gajerun gwamnatoci, rikicin kafa gwamnatin hadaka da sauransu wadanda sdukka suka jefa Kasa cikin matsala.

Tsari da turbar kundin tsarin mulki na 1961 ya kawo ya sanya tsoro sosai yadda bai ba wa ‘yan majalisa karfi ba kuma ya tattara karfinsa ne ga bangaren Shari’a. Tsarin ya janyo juyin mulki da tsoma bakin sojoji a gwamnati, ya ba wa kasashen waje damar katsalandan a Turkiyya, na samar da alkalai da ke aiki da rufaffen tsari tare da zama abu mai hana ci gaba kasa da demokradiyyarta.

Tsarin ya zama mai son tabbatar da abun da ake tafiya a kai, tare da janyo sauya gwamnatoci da yawa da yunkurin kafa gwamnatin hadaka wanda ba ya haifar da da mai ido. Wanne irin tunani ne a ce wata gwamnati da ba ta zo ba, kuma ba ta da tabbas ko tsarin zai dace da ita kokuwa a a, kuma ko zai dace da tsarinta?

Idan ba a yi aiyuka daidai da yadda Turkiyya ke bukata ba, to hakan zai zama kenan ba a magance matsalar katsalandan a cikin gida, da wajen ba a kan gwamnati, ba a tafiyar da barazanar karya tattalin arziki da ake yi daga waje ba, sannan masu rura wutar ta’addanci ba a kawar da su ba.

Matsalolin da aka fuskanta da dama sun zama abubuwan mantawa a lokacin mulkin jam’iyyar AKP. Yadda AKP ta kafa gwamnati ita kadai bayan shekarun 2000 ba abu ne na gama-gari ba, kawai togaciya ce na wannan tsari.

Akwai manyan matsaloli biyu da ke damun yammacin duniya da ma duniyar Musulunci, abun da jama’a suka zamba ya kasance ba shi suke gani a siyasance ba da kuma yadda idan an hau gwamnati a kasa kawo sauyin demokradiyya.

Sabon tsarin shugaban kasar ya tanadi dole ne wanda za a zaba a matsayin shugaban kasa ya kasance ya samu kaso 50+1 na kuri’un da za a jefa wato hakan na nuna kai tsaye damar na hannun jama’a. Wadanda suka ga matsalolin wannan abu da kuma wadanda suka bayar da gudunmowa suna cewa, abun da muka yikuwa daidai ne. A baya wasu na tunanin za su hau mulki ba tare da tunanin wasu jama’ar ba.

Wannan na bayyana cewa, ai Recep Tayyip Erdoğan na son dauwama a kan mulki. Kuma tsarin amfani da majalisa ba zai haifar da matsaloli ba idan ana da shugabanni masu karfi irin Erdoğan. Amma idan muka kalli tarihin Turkiyya za mu ga ba a samun jam’iyya daya da ke ta lashe zabe a lokuta da dama a jere ba kamar ta Etdogan. Wannan nazarar Erdogan ce shi kadai a saboda haka dole ne a yi tunanin bayan sa kuma me zai afku.

Idan aka kuma dubi jam’iyya mai mulki za a ga cewa, tana samun nasarar zabe ba tsare da wata matsala ba, sannan kuma tsarin amfani da majalisa ya fi sauki wajen zabar shugabanni. Amma idan ana son a samar da daumammen zaman lafiya, to kar a bayar da dama ga kasashen waje na tsoma baki a Turkiyya, sai a ba wa ra’ayin jama’a muhimmanci da zaman sa mafi rinjayi musaman a wannan yanki da Turkiyya ta ke ciki kuma idan ana son tabbatar da wadannan abubuwa dole Turkiyya ta samar da canji na siyasa a kasarta.

A hakan abun ya zama mai wahala ga jam’iyyar AKP amma kuma ta yi daidai. Ta hanyar canjin da aka samar ya zama al’umar Turkiyya su ne shugabannin siyasarsu. Masu katsalandan daga kasashen waje da ba su samu yarjewar al’umar kasa ba za su yi rauni matuka. Zai zama a an warware matsalolin da siyasa ta ke janyowa sosai. Daga yanzu ba matsalolin tsarin za mu dinga aunawa ba, matsalolin da aiwatar da tsarin ya haifar za a kalla.

Sakamakon haka, abinda ake jira daga wajen ‘yan hamayya shi ne, ba wai su ce za su kawar da shi ba tare da gwada amfani da shi ba tare da ganin yadda ya ke ba, kamata ya yi su mayar da hankali wajen warware matsalar da aiwatar da tsarin zai iya haifarwa.

Duk da har yanzu ‘yan adawa ba su farga ba, sabon tsarin siyasa ya kawo sauyi ga yadda ake kallon shugabanci. Jam’iyyun da suke kallon matsalolin mutane, suke kallo mai jama’a suke sanyawa da halinsu, a yau sun zama ba matsalolin jama’a suke neman warwarewa ba, ba sa alkawarin yin aiyukan alheri ga jama’a, amma sai suke cewa sabon tsarin da ba su yi amfani da shi ba za su sauya. A mako mai zuwa za mu yi nazari kan sauyin siyasa na wannan sabon tsari da tasirinsa a aiyukan yin zabe da ake yi.

Sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

 Labarai masu alaka