Turkiyya ce kan gaba a yunkurin samar da zaman lafiya a Siriya

An dai ci gaba da gudanar da ka’idojin da aka aminta akan su a yarjejeniyar Astana da aka yi domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Siriya.

Turkiyya ce kan gaba a yunkurin samar da zaman lafiya a Siriya

Ana dai ci gaba da gudanar da ka’idojin da aka aminta akan su a yarjejeniyar Astana da aka yi domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Siriya. Matakan da kasashen samar da lumana da suka hada da Rasha, Turkiyya da Iran suka dauka da kuma aiynar da hare-haren da kasashen Iran da Rasha suka yi a yankunan, sun sanya an samu kwanciyar hankali musanman a yankin Idlib. Kasancewar yadda Idlib ke makwabtaka da Turkiyya ya sanya Turkiyya kasancewa muhimmiyar kasa a yunkurin samar da lumana a yankin. Bugu da kari, hare-haren Firat kalkanı da aka gudanar ya sanya kauda dukkan kalubale da kuma mika yankin ga sojoji amintattu. Matakan da aka dauka dangane da yarjejeniyar Astana domin rage fitunun dake afkuwa a Idlib na da bambanci dana sauran yankunan. Kafa guraren sa ido 12 da Turkiyya ta yi, a yayinda Rasha ta samar da 10 inda kuma Iran ta kafa 7 ya sanya samar da zaman lafiya da rage tashin hankula a yankin, musanman yankunan sanya idon Turkiyya a yankin sun kasance tamkar wasu katangu da suke kare kalubalen sojojin gwamnati ga sojoji masu zaman kansu.            

Akan wannan maudu’in mun sake kasancewa tare da Mal. Yazar Can ACUN dake cibiyar nazarin siyasa da tattalin arziki wato SETA.

Guraren sanya ido da Turkiyya ta kafa sun fuskanci wadansu kalubale, sabili da a dai-dai lokacin da Turkiyya ke kokarin kare iyakokinta kai tsaye, ta tilastu da kuma daukar matakan kauda dukkan ‘yan tada zaune tsaye da kuma samar da zaman lafiya a yankunan Idlib. A kokarin haka, ansha kaiwa manyan motocin Turkiyya hari da bama-bamai dake sintiri a yankin, haka kuma sau da yawa sojojin gwamnatin kasar da kungiyoyin Shi’a da Iran ke goyawa baya su kan kaiwa jami’an tsaron Turkiyya hari  yankunan. Turkiyya dai na ci gaba da aika sojojinta a Siriya domin ita ce kasa tilo da ake ganin yunkurin ta na samar da zaman lafiya a Siriya baiyane.

A dai-dai lokacin da Turkiyya take kokarin shiga tsakanin sojojin gwamnatin Siriya da sojoji masu zaman kansu domin aiyanar da sulhu, tana kuma daukar matakan kauda ta’addanci dake kalubalantar Siriyar baki daya.

Turkiyya wacce ta kauda kungiyar ta’addar DEASH a lokacin hare-haren Firat Kalkani ta kuma dauki matakan kauda kungiyar ta’addar PKK/YPG a yankunan Afrin. Duk da irin wadannan muhimman matakai biyu da Turkiyya ta dauka, ba ta aiyanar da wani yunkurin da zai raba ko mamaye kasar Siriya ba. A yayinda Turkiyya ke kokarin samar da zaman lafiya a Siriya ta na kuma daukar matakan kauda ta’addanci a yankunan baki daya tare da kuma samar da tsaro ga kasarta. A sabili da wadanan matakai, musanman bayan kauda DEASH a hare-haren Firat Kalkani an samu raguwar kaiwa Turkiyya hare-haren ta’addanci da dama, haka kuma hare-haren reshen zaitun da aka gudanar ya sanya kauda kai harin ta’addanci a yankunan tsaunukan Hatay da Amanos. Duk da haka, Turkiyya na ci gaba da kai hare-hare kauda ta’addanci a Iraqi da kuma kalubalantar kungiyar PKK/YPG a arewacin Siriya.

A dayan barayin kuma, ganin yadda Amurka ke ci gaba da haddin gwaiwa da kungiyar ta’addar YPG ya sanya rashin kauda ta’addanci a yankin baki daya da kuma kara haifar da kalubalen tsaro ga kasar Turkiyya. Turkiyya ta jima tana tattaunawa da Amurka akan lamurkan YPG musanman a yankin Membich. Kasancewar yadda Amurka ta ki cika alkawarinta na za ta janye mambobin YPG daga yankin bayan ta mallaki yankin ya sanya  dangantaka yin tsami tsakanin Turkiyya da Amurka wadanda dukkaninsu mambobin kungiyar NATO ne.

A lokacin da Rex Tilleron ke ministan harkokin wajen Amurka ya ziyarci Turkiyya inda ya tattauna da takwaransa akan lamurkan Membich har aka fahimci juna akan wasu lamaurkan, amma bayan cireshi da shugaba Trump ya yi da kuma nada Mike Pompeo a matsayinsa, lamurka sun yi tsaye. Duk da haka kalaman Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu a ‘yan kwanakin da suka gabata na nu ni da cewar kasashen biyu zasu tattauna akan yadda za’a bulluwa lamarin yankin Membich. Bayan kalaman na Çavuşoğlu kafafen yada labaran cikin gida sun bayyana cewar ‘yan kungiyar YPG sun fara shirin kauracewa daga yankin. Hakika idan kasashen biyu suka fahimci juna suka aminta akan kauda kungiyoyin ta’addanci daga yankin Membich zasu yi hadaka wajen samar da zaman lafiya a yankin da kuma kafa jami’an tsaron da zasu kula da yankin. Amma duk yadda kasashen biyu suka samar da lumana a Membich akwai wahala su iya samar da tsaro a gabashin Firat, sabili da ‘yan ta’ddar da zasu yi kaura daga Membich za su iya komawa ne a gabashin Firat, sabili da haka akwai bukatar Amurka da Turkiyya wadanda suke dukkaninsu mamabobin NATO ne su ci gaba da hadaka da musayar bayanai domin samar da zaman lafiya a dukkanin yankunan Siriya dama yankunan kasashen baki daya.

Wannan sharhin Malam Yazar Can ACUN ne daga Cibiyar Nazirin Siyasa da Tattalin Arziki wato  SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.

 Labarai masu alaka