Me ya sa zaben ranar 24 ga watan Yuni yak e da muhimmanci?

Alla kulli halin zaɓen ranar 24 ga Yuni ba zai kasance abin da kafafen yaɗa labarai suke aiyanarwa ba, ba kuma zai kasance ra'ayin wasu ƙungiyoyin dake da niyyar biyan buƙatunsu ba, amma zaɓe ne da zai bayyanar da haɗin kai da ra'ayin al'umar Turkiyya.

Me ya sa zaben ranar 24 ga watan Yuni yak e da muhimmanci?

Alla kulli halin zaɓen ranar 24 ga watan Yuni ba zai kasance abin da kafafen yaɗa labarai suke aiyanarwa ba, ba kuma zai kasance ra'ayin wasu ƙungiyoyin dake da niyyar biyan buƙatunsu ba, amma zaɓe ne da zai bayyanar da haɗin kai da ra'ayin al'ummar kasar Turkiyya baki ɗaya.

Zaɓen da za'a gudanar ranar 24 ga watan Yuni, zai baiwa Turkiyya damar canjawa zuwa tsarin shugaban ƙasa da kuma inganta lamurkan tattalin arziki da siyasar kasar.

Zaɓen raba gardamar da aka gudanar a shekarar bara ya bayar da damar fara mulkin tsarin shugaban ƙasa akan tafarkin unitary, wanna tsarin ya banbanta da irin na Amurka saboda rashin tsarin Federal, wanna tsarin ya so yayi kamada na Faransa amma kuma babu firaminista. A wannan tsarin ƴan majalisu zasu fara yin doka, kuma za'a raba ikon ƙasar tsakanin zabbabun shugabanni, ƴan majalisu da hukumomin Shari'a. Tsarin zai baiwa shugaban kasa damar ɗaukar ministocin sa daga faɗin ƙasar, haka kuma ma'aikatan Shari'a zata kasance mai zaman kanta, a takaice dai za'a tsarin zai kuɓutar da Turkiyya daga irin matsalolin da ake samu idan an kafa gwamnati haddin gwiwa.

Duk da an samu ƴan takarar shugaban kasa da dama, shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya fi sauran ƴan takarar da daraja mai tazara. Sabili da haka zai lashe zaben tun a turmin farko. Erdoğan ya samu wannan martabar ne kasancewar irin aiyukan inganta rayuwar al'ummar kasar da ya yi cikin shekaru 16.

Hakan ya faru ne saboda irin muhimman aiyukan da shugaba Erdoğan ya aiyanar kamar bunƙasar da tattalin arziki, ƙaruwar kuɗaɗen shiga, habbaka kasuwancin kasa, gina sabbin jami'o'i da guraren samar da ilimi, kare hakkokin ƙananan ƙabilu da suka haɗa da Kurdawa, Alebi da armeniyawa. Hakan ya sanya al'ummar kasar kauda dukkan yunkurin juyin mulki da aka so a yi masa a shekarun 2007, 2010 da ma wadanda ƴan ta'addar FETO suka yi yunkurin yi a ranar 15 ga watan Yuli 2016.

Babban akidar shugaba Erdoğan ita ce gudanar da aiyuka ba tare da nuna banbanci ba ko wace iri, wannan kyakkyawar ɗabiar yana daya daga cikin abubuwan da suka bunkasa farin jinin Erdoğan a zaben da aka yi dama wanda za'a yi a halin yanzu. A matsayin sa na shugaban jam'iyya mai sassaucin ra'ayi yana kokarin haɗa kan dukkanin ƙabilu da bangarorin ƙasar, duk da ba za'a ace dukkanin ƴan ƙasar na goyon bayan sa ba, matakan da ya dauka kyawawa ababe ne da kusan kowa ya shaida.    

Rashin nuna wariya da bambanci da kuma kawar da kai da asali, al’adu ka kabilar mutane wajen mu’amala da su ne falsafar sayasar Erdoğan.     Ana ganin alamun haka a tarukan kamfe na zabe da ake gudanarwa. Hakan ya sa a wannan gaba ba a iya kwatanta shi da abokan hamayyarsa. Shugaban jam’iyyar dama ta tsakiya amma kuma maimakon a gan shi da halayyar fifita wani yani kotunani, sai ga shi ya rungumi dukkan sassan al’uma. Hakika a siyasa ba za a ce kowa ya gamsu da manufofin Erdoğan ba amma kuma ya samu karbuwa a wajen jama’a baki daya.

Masu hamayya da shi suna suka tare da nuna rashin amincewa da duk wani abu da ya fada inda suke zama masu adawa da duk wani mataki da ya ce zai dauka. Wannan abu bai yi tasiri a wani zamani ba haka kuma a ranar 24 ga Yuni ba zai yi ba. Turkawa na da basirar bambance zancen gaskiya da na shirme kokarya. Jama’a suna fahimta da zarar wani dan siyasa ya yi alkawarin wani abu na karya ko ya ce zai yi abinda ba zai iya aikatawa ba. Sun gane wasan sosai.

Wannan gaba ce da a kowanne lokaci kafafan yada labarai na Yammacin Duniya suke mayar da hankali kan Turkiyya idan zabuka sun zo. Suna ta hasashen cewa, Erdoğan zai fadi zabe nan da wani dan lokaci. Amma kuma sai ci gaba da yin nasara ya ke yi. Suna ta kokarin nuna ‘yan adawa a matsayin sauyi amma kuma sun gaza fahimtar yadda al’amuran siyasa suke tafiya a Turkiyya. Babu togaciya suna kitsa karya game da Turkiyya suna yadawa duniya amma hakan ya sanya Erdoğan na ci gaba da nasara a zabukan Turkiyya da ake yi. Wannan al’ada tana cutar da aikin jarida.

Idan za a dinga nuna duk wani abu da ya shafi Erdoğan a matsayin mara kyau to wanna ba aikin jarida ba ne. Duk da wannan bata suna da ake yi wa Erdoğan wanda a baya ma an yi amma sai sake habaka da nasara ya ke yi. Wasu masu nazari na nuna karfin shugabancin Erdoğan da iko a siyasance da ya ke da shi matsayin kama karya saboda ‘yan kasa sun san me shugaba Erdoğan ya yi musu.

A kwanaki masu zuwa, zan so na ga irin martanin da kafafan yada labarai na duniya za su mayar game da alkawarin samar da wuraren shakatawa na al’uma guda 30 manya da kuma wasu 5 kanana. Sannan za a ga me za su ce kan alkawarin mayar da fiin tashi da saukar jiragen sama na 3 zuwa wani babban wajen shakatawa wanda sai ya fi na Central Park da ke birnin New York girma nnkin ba ninkin har sau 8. Wannan wurin shakatawa zai kai tsayin kilomita 11. Zai kuma fi hayde Park na Landan girma har sau 3. Wannan aiki ne na korantar da Turkiyya mai tarihi. Ga dukkan alamu kafafan yada labarai na yammacin duniya za su yi mummunar fassara kan wannan aiki. Mu kuma a wannan lokaci na makwanni 4 za mu tsaya mu kalli yadda al’amuran siyasa za su kasance ba masu amfani da aikin jarida wajen yin wasansu.

Wasu da suke kiran kansu kwararrun Turkiyya za su soki Erdoğan tare da yabon abokan hamayyarsa. Amma in haka ne to ya kamata su yi amfani da gaskiya yadda ya kamata wajen yin hakan. Yın rubutu mummuna game da tattalin arzikin Turkiyya, yabo da daukaka kungiyoyin ta’adda na PKK da FETO tare da nuna ma’asumancin yaran Gulen, kirkirar karya game da shugaba Erdoğan, ba za su hana a ba wa Erdoğan kuri’a a ranar 24 ga watan Yuni ba. Amma a duk lokacinda Turkiyya ta zama labaran kafafan yada labaran kasashen yamma, to ana kaskantar da aikin jarida da kimarsa.

Zaben 24 ga watan Yuni yana da muhimmanci ba wai ga Turkiyya kadai ba, da Gabas ta tsakiya, turai da Amurka inda za a samu habakar tattalin arziki, bunkasa da tsaro a Kasar. Karfin Turkiyya wadda kawa ce ta NATO karfin kawayenta ne. kuma yadda za a kalli wasu hadurra da ke fuskantar turkiyya haka ya kamata a kale sui dan suka bulla a kasashen NATO.

Ya kamata a san ba wai wasu kafafan yada labarai ne za su yanke hukunci a ranar 24 ga watan Yuni ba, jama’ar Turkiyya ne da kansu.

Rubutun Ibrahim Kalin Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya.

 Labarai masu alaka