Ga wa ko me ya sa ake batun "Musulunci Mai Sauki?

Sharhin Shugaban Tsangayar Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara Farfesa Kudret Bulbul.

Ga wa ko me ya sa ake batun "Musulunci Mai Sauki?

Matsalolin Kasashen Duniya: 22

Masu karatu barkanmu dai tare da sake kasnacewa a cikin shirin Matsalolin Kasashen Duniya. Daga lokaci zuwa lokaci hukumomin leken asiri na kasashen duniya na iya shiga tattaunawar gangan don kauce wa batu na gaskiya. In haka ne tarihi ya nuna mana cewa, rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya, kuma ranar wanka ba a boyen cibi.

Babban misalin da za a iya bayarwa kan wannan batu shi ne cece-kuce da muhawarar da ake yi kan “Musulunci Mai Sauki”. A lokacinda Yamma ke fama da matsalolin, a lokacin da yammacin duniya da ke fuskantar barazana mai tsoratarwa ga insaniyya, amma an mayar da hankali wajen kakaba muhawara da mujadala kan batun “Musulunci Mai Sauki”. Kafin yakin duniya na biyu Yammacin duniya bai kall, irin barazana da Yahudanci ke yi ba, haka ma a yanzu ba a kalli irin barazanar nuna kyamar baki da Musulmai ba sai al’uma suka bige da tattauna wa batun “Musulunci Mai Sauki”.

Wasu Faransawa Yahudawa su 300 saboda rashin kunya wai suna cewa, Alkur’ani na bayyana ko umartar Musulmai da su kyamaci Yammacin Duniya da Yahudawa a saboda haka akwai bukatar a yi masa kwaskwarima. Wadannan Faransawa sun sanya hannu kan wannan bukata tasu. Amma wadannan kasashe da suke a duhu sun yi shiru kan yadda Amurka ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa Kudus da yadda Isra’ila ta dinga harbi da kashe Falasdinawa da jikkata wasu dubunnai. Sun yi shiru kan wannan kisan kare dangin da aka yi wa Falasdinawa.

Baya ga wannan akwai wani abu na nuna kyama ga Musulmai a duniya?. An rasa wani mai hankali da zai bayyana cewa, ana zaluntar wadannan mutane a yankunansu. Kuma ana amfani da sunan Musulunci Mai Sauki wajen karkashe su tare da take hakkokinsu da mamaye kasarsu. Kamata ya yi a kira wadannan aiyuka na ta’addanci ba wai sunan neman bukatar Musulunci Mai Sauki ba. Amma kuma yadda ake samun hare-hare daga Kiristoci a ‘yan shekarun nan babu mai kira da samar da Kiristanci Mai Sauki. Kuma ba a nuna bukatar Yahudanci Mai Sauki duba da tsawon shekaru da aka dauka Isra’ila na zaluntar Yahudawa, mamayarsu da karkashe su. Ba wani da yake muhawara kan wannan batu.

Idan muka kalli batun aa ikace za mu ga cewa, a lokacin da ake fadin “Musulunci Mai Sauki” ba wai ana nufin yaki da ta’addanci ba ne. Ana son kawai a nuna yadda ake da hanya mai sauki wajen magance duk wani Addini na masu rinjaye koma daga wanne bangare suke.

A aikace idan aka kalli wadannan Hukumomin Leken Asiri ne kuma su wa suka mara wa baya, za a ga cewa, bullo da batun Musulunci Mai Sauki na bayar da dama a mallake tare da sace dukokin waje da na karkashin kasa mallakar Kasashen duniya, karkashe su, mamayar su tare da zaluntar su ta hanyar biyan bukatun ‘yan mulkin mallaka. ‘Yan mulkin mallaka na kai komo a Gabas ta Tsakiya don amfanin kansu, amma ana nuna tunanin mutanen da ke yankin ne ya zama laifi da barzana.

Me ya sa ko kuma mene ne dalilin da ya sanya jama’ar yankin bayar da damar yi musu mulkin mallaka, to za a kalli batun ta fuskar matsalolin da suke da su. Matsalolin kansu ne suka ba wa ‘yan mulkin mallaka dama a kansu.

Idan aka kalli irin makaman da ‘yan ta’addar FETO, PKK/PYD suke da shi da masu goya musu baya, za a ga cewa, wadannan kungiyoyi na ta’adda suna da alaka da Hukumomin Leken Asiri na Kasashen Yamma.

Wasu kasashen yamma yadda ba za su amince kan hakkokinsu ba amma suna hakilancewa wajen kaka gida a kasashen Musulmi. Kasashen Yamma a Gabas ta Tsakiya banda a Isra’ila babu wata kasa da suke taimakawa wajen dabbaka demokradiyya. A Masar da aka kashe mutane da dama suna ganin babu wata matsala. Kuma Wasu da suke mulkin kama karya ba su da matsala. Sun amince da su a matsayin mutanen kirki. A karkashin wannan a yanzu a wata kasa ma mata na tuka mota inda ake ta yabonsu, sannan ana ta suka, kyara da kage ga Turkiyya wadda ta fara yin zabe a shekarar 1876 kafin Kasashen Yamma sannan ta samu ci gaba a 1934 kafin Kasashen Yamma su samu.

Idan aka kalli manufofin wasu Kasashen Yamma a Gabas ta Tsakiya za a ga ba wai su ne silar zaman lafiya, tarihi, al’uma da wayewar yankin ba, kwai suna samar da tunani irin na wasu bangarori da ke nuna bambancin mazhabanci da na asali. Watak,la sakamakon haka ne ya sanya kamar yadda ya ke a Masar da wasu Kasashen Gulf da ke karkashin Sarakuna suke ci gaba da wanzuwa a kan mulki duk kn son hakan da jama’arsu ke yi. Amma kuma saisuke shaidantar da Turkiyya da shugabanta Recep Tayyip Erdoğan wanda al’uma suka zaba kuma suke son sa.

Wasu kasashen Yamma da cibiyoyinsu idan aka kalli dabi’u da halayensu za a ga cewa, abinda suka fahimta daga Musulunci Mai sauki shi ne su zalinci jama’a amma sun manta su ma suna bukatar hali Sassauka. Suna cewa kasashe da gwamnatocin da suka yi shiru kan irin mamaya da zaluncin da ‘yan mulkin mallaka suke musu su ne “Mai Saukin ra’ayi” amma wadanda suka nuna ba sa son wannan mamaya sai su dinga kiran su da suna “Masu kama karya” a wajen Kasashen Yamma mai sauki ra’ayi shi ne mai zalunta da ha’İntar jama’arsa.

Wasu cibiyoyin kasa da kasa, suna bayar da taimako ga wasu kngiyoyin ta’adda da ba su da asali inda suke ganin wannan shi ne abin da za su samu nasara a kai. Idan haka ne,  kamata ya yi a ce irin ‘yanci da wanzuwar jama’a da ake da su a Yammacin duniya ya dinga taimakawa na Gabas ta Tsakiya. Yadda wasu kasashen duniya ke taimakawa ‘yan ta’adda abu ne mummuna da ba zai haifar da da maiido ba. Idan aka kalli haka, a yau a kasashen Balkan da Gabas ta Tsakiya a tsaknin bangarorin da suke rikici da juna Turkiyya a matsayin “Sabuwar Daular Usmaniyya” na taka muhimmiyar rawa wajen sasantawa da wanzar da zaman lafiya. Akwai rawar da Turkiyya za ta taka sosai.

Sharhin Shugaban Tsangayar Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara Farfesa Kudret Bulbul.Labarai masu alaka