Rikincin Qatar da kasashen Gulf: Kaikayi ya koma kan mashekiya

Takunkuman siyasa, soja da tattalin arzikin da Haddadiyar Daular Larabawa da Saudiyya suka sanyawa Qatar ya fara komawa kansu, a takaice dai munce kaikayi ya fara komawa kan mashekiya.

Rikincin Qatar da kasashen Gulf: Kaikayi ya koma kan mashekiya

Kimanin shekara daya kenan da aka datse kafar sadarwar  kanfanin dillancin labaren Qatar tare da yada wata tattaunawar karya da akace wai anyi da sarkin Qatar. A dai-dai wannan lokacin ne Haddadiyar Daular Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya da gudunmowar Amurka sunka sanyo Qatar din gaba. Wannan haddin gwiwar da suka yi domin kange lamurkan soja, siyasa da tattalin arzikin Qatar, ya so ya tilastawa Qatar din mika wuya garesu.             

Akan wannan sabowan maudu’in mun sake kasancewa tare da Mal Yazar Can ACUN dake Cibiyar Nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA.

Idan muka duba, zamu ga cewar wannan kalubalnatar Qatar din ya biyu bayan taron kasa da kasa da aka gudanar a ranar 21 ga watan Mayun shekarar 2017 a Riyad a lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya ziyarci Saudiyyar. Tabbacin samun goyon baya daga Trump ya sanya masu suna Muhammad guda biyu da suka hada da Bin Salman da Bin Zayed daukar matakin kalubalantar Qatar. Suna dai kallon Qatar a matsayar kalubale ga manufofin dasu da Isra’ila ke neman aiyanarwa a gabas ta tsakiya, a sabili da hakan ne suka yanke hukuncin sanya Qatar din gaba. A lokacin juyin juhanin kasashen larabawa, Qatar  da kamar su Turkiyya masu karfi a yankin sun taimakawa wadanda ke neman kawo sauyi a yankunan ta hanyar amfani da kafafen yada labarai da kuma gudunmowar kudade. Abin ya kasance daya daga cikin dalilan da akaso a kalubalanci Qatar din da shi.

Idan muka dubi lamurkan da suka afku cikin shekara daya zamu ga cewar duk da irin kalubalantar da suka yiwa Qatar din lamarin bai yi wani tasiri akan ta ba. Gudunmowar da ta samu daga kasashe musanman Turkiyya ya sanya dukkan irin kalubalantar ta da akaso ayi bai yi wata tasiri ba, har da ita kanta ma Amurka ta fara dawowa daga aniyarta ta farko akan Qatar din. Takunkumin da Haddadiyar Daular Larabawa da Saudiyya suka sanyawa Qatar din ya fara komawa kansu, a takaice dai munce kaykayi ya fara komawa kan mashekiya.

Daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya aka kalubalanci katar din shi ne nemanta da ta yanke yarjejeniyarta na soja da kasar Turkiyya da kuma mayarda sojojin Turkiyya dake kasanta zuwa kasarsu. Babban dalilin hakan dai shi ne, sun fahimci matukar akwai sojojin Turkiyya a Qatar, ba zata kasance lomar da za’a iya hadiyewa nan take ba, bugu da kari horar da sojojin Turkiyya ke yiwa sojojin Qatar din zai iya sanya karfafan Qatar din a yankin nan zuwa gaba. Muhammad din dai guda biyu da kuma Isra’ila na kalon karfin siyasa da  sojojin Turkiyya a matsayin kalubale a yankin, sabili da bukatunsu da suke da niyyar aiyanarwa a duniyar musulmi tun daga Falasdin zuwa Qatar ba zai yiwu ba matukar Turkiyya na daukar matakai a yankin. Akan hakan ne suka nemi Qatar din da ta fara yanke yarjejeniyar sojanta da Turkiyya. Turkiyya da Qatar dai sun sanya kafafuwan hagu inda suka yi fatali da wannan bukatar a yayinda Turkiyya ta kara kwarin gwiwar siyasa da soja a yankin, lamarin da ya sanya rashin tasirin duk matakan da aka so a dauka akan Qatar din.

Turkiyya dai ta fahimci dukkan irin matakan da Saudiyya da ma Haddadiyar Daular Larabawa ke neman dauka a yankin. Kalaman jakadan Haddadiyar Daular Larabawa a Amurka Yusuf al Uteybe na nuna cewar Haddadiyar Daular Larabawan tare da haddin gwiwa da Isra’ila na daukar matakan kalubalnatar yunkurin Turkiyya a kasashen Libya, Somaliya da Siriya.

Turkiyya dai bata damu da duk wata bakar farfagandar da ke faruwa a cikin Haddadiyar Daular Larabawan ba, sai dai ta fara mayar da martani a kan ababen da take neman aiyanarwa a Somaliya. Turkiyya dai kasace mai kwari a fanonin siyasa da soja wacce keda aniyar samar da lumana a yankin kamar a Iraqi da Siriya. Sabili da haka baya ga Qatar akwai sojojinta a kasashe irinsu Somaliya, hakika zata ci gaba da kare dukkanin wasan kwanto baunar da ake yiwa duniyar musulmi da kuma Qudus.

Wannan sharhin Mal Yazar Can ACUN ne dake Cibiyar Nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA daga nan Ankara babban birnin Turkiyya.

 Labarai masu alaka