Turkiyya ta daura damarar kare hakkokin Falasdinawa

Mayarda ofishin jakadancin Amurka na kasar Isra’ila daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus da kuma zaben kasar Iraqin sun kasance lamurka biyu a gabas ta tsakiya da suka taba Turkiyya da duniya baki daya.

Turkiyya ta daura damarar kare hakkokin Falasdinawa

A halin da ake ciki yanzu afkuwar muhimman lamurka biyu a gabas ta tsakiya sun shafi  Turkiyya da ma duniya baki daya. Na farko dai shi ne canja ofishin jakadancin Amurka na kasar Isra’ila daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus lamarin da janyo budewa fararen hular dake zanga-zangar kalubalantar hakan wuta da ya haifar da mutuwar Falasdinawa 60 da kuma raunana 2770, lamari na biyu kuwa shi ne nasarar da shugaban Shi’ar kasar Iraqi Mukteda as Sadr ya samu a zaben da aka gudanar a Iraqi            

Akan wannan maudu’in na mu mun sake kasancewa tare da Mal. Yazar Can ACUN dake Cibiyar Siyasa da Tattalin Arziki wato SETA anan Turkiyya.

Bayyana mayar da ofishin jakadancin Amurka ta kasar Isra’aila daga birnin Tel Aviv zuwa Qudus da shugaba Donald Trump ya yi, ya haifar da gudanar da zanga-zanga da dama a fadin duniya. Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta kalubalanci wannan yunkurin na Amurka lamarin da ya samu amincewar mafi yawancin kasashe. Duk da haka Amurka ta ci, gaba da aniyarta na tabbatar da Qudus a matsayar babban birnin Isra’ila yunkurin da kasashen duniya suka yi tir da shi. A cikin wannan yanayin ne Turkiyya ta gudanar da taron Kasashen Tarrayar Islama a inda suka nuna rashin amincewarsu akan yunkurin Amurkan, lamarin da ya tabbbatar da kalaman shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan da cewa “Duniya ta  fi biyar girma”

Duk da wadanan matakai shugaba Trump bai canja ra’ayinsa na mayar da Qudus babban birnin Isra’ila ba, a inda yaci gaba da dadadawa masu akidar Abenjelism dake neman mayar da Qudus birnin Isra’ia rai, hakan ya aiyana ne saboda akwai masu irin wannan akidar da yawa acikin majalisar zartawar shugaban na Amurka. A ‘yan kwanakin da suka gabata a yayinda Amurkan ke bude ofishin jakadancinta ta Isra’ila a Qudus da yawan Falasdinawa sun fita suyi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu a Gaza, Duk da zanga-zangar sun gudanar da ita cikin lumana bai hana sojojin Isra’ila bude musa wuta ba, lamarin da ya haifar da mutuwar Falasdinawa 60 da kuma raunana wasu 2770.

A dai-dai lokacin da ake kashe Falasdinawa da raunanasu, diyar shugaba Trump da surukinsa suke gudanar da bukin bude sabuwar ofishin jakadancin Amurkan a Qudus. Duk shaidon bidiyo da aka fitar akan cin zalin da Isra’ilawa ke yiwa Falasdinu, Amurka na kokarin ganin laifin Hamas akan lamarin. Hakika, Amurka ta nuna tafi bukatar cimma burinta akan kare hakkokin Falasdinawa da suaran fararen hula.

Turkiyya ce dai ta kasance kasa tilo dake yunkurin daukar matakai akan kare hakkokin Falasdinawa a duniya. Turkiyya ta aiyanar da kwanaki uku domin zaman makoki akan lamarin, haka kuma majalisar kasar ta yi Allah wadai da lamarin a yayinda kuma ta janye jakadojinta daga Isra’ila da Amurka tare da korar jakadan Isra’ila daga kasarta

Daga cikin muhimman lamurkan da suka taba kasar Turkiyya a halin yanzu kuma shi ne zaben kasar Iraqi. Yankunan Musul, Felluce da Anbar da suka kasance cikin kalubalen kungiyar ta’addar DEASH sun samu zaman lafiya, haka kuma bayan zaben raba gardamar arewacin Iraqi rigingimun yankunan Kerkürk da Sincar sun ragu matuka a yayinda aka yi nasarar kubutar da yunkunan, lamarin da ya kara armashin zaben da aka gudanar a kasar. Duk da haka, kasancewar kaso 44 daga cikin dari ne kachal suka fita kada kuri’a na nuna cewar har ila yau Iraqi na fama da matsalar tsaro a kasar.

Daga cikin ‘yan takara a zaben dai sun hada da firaministan Iraqi Haydar al-Ibadi, tsohon firaminista Nuri el Maliki, shugaban shi’a Mukteda as Sadr da kuma Hasdi Shabi. Kawancen shugaban sunni Usame en –Nuceyfi  da kuma kawancen shugabanin shi’a, da Ammar el Hekim ya jagoranta sun kasance lamurkan da suka nuna alkiblar zaben.

Daga cikin wadanda Iran ta goyawa baya a zaben sun hada  da tsohon firaministan Iraqin Nuri al Maliki da Hashdi Shabi, a yayinda Haydar el İbadi da Mukteda es –Sadr suka kasance kusa da Amurka da Saudiyya. Hukumar zaben ta bayyana Mukteda as –Sadr a matsayin wanada ya zo na daya, Hashdi Shabi na biyu, na uku kuwa firaministan kasar Haydar el- İbadi, a yayinda tsohon firaministan kasar Nuri al Maliki ya zo na hudu. Shugaban shi’a Mukteda da ya zo na daya ya bayyana a shainsa ta sadar da zumunta irin kawancen da yayi da wasu shugabanin a inda ya tabbatar da kafa gwamnatin hadin gwiwa da shugabanin shi’a da suka hada da Ammar al Hakim Hikmet Akımı, İyad Allay da sauran kuniyoyin kurdawa da suka hada da Goran. Da kuma ma wasu shugabanin sunni da suka hada da Usame en –Nuceyfi, Halid el-Ubeydi da kuma Haydar el İbadi Nasir.

Bayan wannan zaben dai ana hasashen karfi da damar da Iran keda shi a Iraqi zai ragu, musanman yadda ba’a zaton kasancewar tsohon firaministan kasar Nuri el Maliki da Hashdi Shabi daga cikin wadanda za’a kafa gwamnatin dasu. Duk da haka, wasu na ganin, muhimmancin Iran a Iraki zai ci gaba musanman a fannonin soja ganin yadda jami’an tsaro mafi karfi na biyu a kasar na karkashin jagorancin Hashdi Shabi ne, hakan ka iya baiwa Iran din damar katsa landar a harkokin na Iraqi.

Zaben kasar Iraqin na tabbatar da Amurka da Saudiyya sun fara nasara akan yunkurinsu na mallakar harkokin gabas ta tsakiya, shugaban shi’a Mukteda as –Sadr da ya lashe zaben da ya kasance a da yana kalubalantar Amurka, ya zaman abokin hurdar Amurka da Saudiyya a halin yanzu. Haka kuma kasancewar  İbadi ya yi kawance da Amurka wajen yaki da DEASH da kuma  kai ziyara a Saudiyya a ‘yan kwanakin da suka gabata na kara tabbatar da cewa kawancen Amurka da Saudiyya ya kasance lamarin dake tafiyar da harkokin kasar Iraqi.

Wannan zaben dai yana da muhimmanci ga kasar Turkiyya, saboda hakan zai bata damar kawance da gwamnatin kasar domin karfafaf yaki da ta’addancii a yankunan baki daya. Rundunar sojan Turkiyya zasu yi hadaka da na Iraqin domin ci gaba da fattatkar kungiyar ta’addar PKK da kwarin gwiwa. Haka kuma Turkiyya zata ci gaba da kawancen da ta hada da Iraqin musanmman a yayin gudanar da hare-haren Firat Kalkani da hare-haren reshen zaitun domin kauda ta’addanci a yankunan.

Wannan sharhin Malam Yazar Can ACUN ne dake Cibiyar Nazarin Siyasa da Tattalin Arziki wato SETA daga nan Ankara babban birnin Turkiyya.

 Labarai masu alaka