Turkiyya zata inganta harkokinta na cikin gida da waje

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan da jam'iyyarsa ta AK Parti sun bayyana alƙawuran da zasu yiwa al'ummar ƙasar idan suka lashe zaɓen da za'a gudanar a ranar 24 ga watan Yuni.

Turkiyya zata inganta harkokinta na cikin gida da waje

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan da jam'iyyarsa ta AK Parti sun bayyana alƙawuran da zasu yiwa al'ummar ƙasar idan suka lashe zaɓen da za'a gudanar a ranar 24 ga watan Yuni. Alƙawuran sun haɗa da inganta fannonin tattalin arziki, lafiya da harkokin cikin gida. Haka kuma ajandar tana kunshe da lamurkan dangantakar Turkiyya da sauran ƙasashen.        

Mun sake kasancewa tare da malam Yazar Can ACUN dake Cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA.

Haƙiƙa, daya daga cikin lamurkan da zasu ja ragamar dangantakar Turkiyya da kasashen ketare, shi ne yaƙi da ta'addanci. Bayan yunkurin juyin mulkin 15 ga watan Yuli, shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya lashi takobin yaƙar ta'addanci cikin gida da waje. Da farko dai, Turkiyya tayi nasarar ƙaddamar da hare-haren Firat Kalkanı inda ta ƙalubalanci ƴan ta'addar DAESH, daga bisani kuma ta fara aiyanar da hare-haren reshen zaitun da haɗin gwiwar sojojin Siriya masu zaman kansu inda suka kauda kungiyoyin ta'addancin PKK/YPG daga yankin Afrin dake ƙasar Siriya.

Hare-haren Firat Kalkanı bai ɗauki tsawon lokaci ba saboda irin sabbin tsarukan da aka dauka a yayin fafatawa da ƴan ta'adda. Haka kuma jami'an tsaron Turkiyya sun dauki matakan kauda hare-haren ta'addanci a cikin ƙasar, sun kuma kauda ƴan ta'addar PKK-YPG daga tsaunukan Amanos dake yankin garin Hatay a ƙasar Turkiyyar.

 Ajandar da shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan ya fitar na nuni da cewa bayan zaɓen shugaban kasa da za'a gudanar a ranar 24 ga watan Yuni, za'a sauya tsarin yaƙi da ta'addanci, ala kulli halin za'a ƙara ƙarfin gwiwa a yaƙin da ake gudanar wa da kungiyar ta'addar PKK a lraqi, haka kuma ana hasashen za'a dauki sabbin salo a fagen yaki da ƴan ta'addar YPG-PKK a arewacin Siriya.

Ajandar da shugaba Erdoğan ya fitar na kuma nuni da cewa bayan zaɓen shugaban kasa, Turkiyya ba zata riƙi kowa a matsayar uwargijiya ba, ba kuma zata zama uwargijiyar kowa ba. Wannan matakin da baiwa; da yawan ƙasashen yamma daɗi ba na bayyana cewar Turkiyya zata duƙufa wajen cimma burinta a faɗin duniya ba tare da dogara ga kowa ba. Shugaba Erdoğan ya jaddada aniyar Turkiyya na zama ɗaya daga cikin manyan kasashe a fadin duniya akan tafarkin da ba zata amince da ko wacce ƙasa ta hakince lamurkanta ba, ba kuma zata hakince harkokin ko wacce ƙasa ba, domin dangantakar da Turkiyya ke yi da sauran ƙasashe bana jari hujja ko mulkin mallaka bane, misali tana gudanar da hurɗar daidaito da bada tallafi ga ƙasashe masu tasowa musamman kasashen Afirka. Kasancewar yadda Turkiyya ce tafi bayar da kaso mai tsoka ga tallafawa ƙasashe maso tasowa idan aka yi la'akari da yawan kuɗaɗen shigarta na tabbatar da cewa Turkiyya na taka rawar gani a kan dangantakar inganta rayuwar bil adama a fadin duniya.

Turkiyya zata ƙarfafa harkokinta da ƙasashen ketare ta hanyar janye jikinta daga dogaro ga ko wacce ƙasa tare da ɗaukar kwararan matakai da suka dace. A wannan barayin za'a inganta kanfunan tsaron cikin gida kamar yadda shugaba Erdoğan ya bayyana a ajandarsa. Kanfunan tsaron kasar Turkiyya sun habbaƙar da kayayyakin da suke fitarwa zuwa ƙasashen waje da kaso 90 cikin ɗari daga shekarar 2011 zuwa yau, hakan ya sanya Turkiyya ta zama ƙasa ta 18 a cikin jerin ƙasashen da suka fi sayar da makamai a duniya. Hakan ya kuma sanya Turkiyya rage dogaro ga makaman ƙasashen waje daga kaso 80 zuwa 30 cikin ɗari. Ana dai nazarin cewar kanfunan tsaron kasar Turkiyya zasu ƙara habbaka a nan gaba. Musamman yadda Turkiyya ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe shida a duniya da ke iya ƙera jirage marasa matuƙa. Haka kuma alwashin da shugaba Erdoğan ya sha na cewar Turkiyya zata fara ƙera tankokin yaƙi marasa matuƙa na tabbatar da cewa Turkiyya ta kama hanyar zama jaruma daga cikin jaruman kasashen duniya. A takaice karfafa kanfunan tsaron kasar Turkiyya lamari ne da zai karfafa kasar baki ɗaya, Turkiyya wacce ta inganta matsayin hurɗar kasuwancin makamai tsakaninta da abokanta, ta samu mazauna a cinikayyar makamai a kasuwan duniya.

Turkiyya dai tuni ta fara fitar da motocin yaƙi zuwa ƙasashen Afirka, gulf, Asiya ta tsakiya da Malaysia. Haka kuma baya ga sayar da jiragen yaƙi masu saukar ungulu kirar ATAK ga Pakistan, Turkiyya ta sayarwa Qatar da jiragen yaƙi marasa matuƙa kirar Bayraktar TB2. A ƙoƙarin bunƙasar da tattalin arzikin Turkiyya an ƙarfafa fannonin bincike akan hakan tare da kuma ƙara gwarin gwiwa domin kyautata zamantakewar ƙasar Turkiyya da sauran ƙasashe.

Wannan sharhin Mal Yazar Can ACUN ne dake Cibiyar siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.Labarai masu alaka