Manyan kasashen duniya sun mayar da Siriya fagen gwajin karfinsu

Ƙasashe masu ƙarfi a duniya dama na yankunan Siriya sun mayar da Siriyar wajen gwada karfinsu, hakan ya biyo bayan faruwar rikicin cikin gidan ta Siriya a sanadiyar ƙalubalabtar gwamnatin Asad da al'umar ƙasar suka fara a shekarar 2011.

Manyan kasashen duniya sun mayar da Siriya fagen gwajin karfinsu

Ƙasashe masu ƙarfi a duniya dama na yankunan Siriya sun mayar da Siriyar wajen gwada karfinsu, hakan ya biyo bayan faruwar rikicin cikin gidan ta Siriya a sanadiyar ƙalubalabtar gwamnatin Asad da al'umar ƙasar suka fara a shekarar 2011, a maimakon samar da demokradiyya wannan yunkurin ya haifar da yaƙin basasa a Siriyar. A daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin ta'addanci a bangare ɗaya ta kasance kuma fagen da manyan ƙasashen duniya dana yankin ke yakar juna a kaikaice. Baya ga manyan ƙasashe dasuka haɗa da Rasha, Amurka, lngila da Faransa ƙasashe masu ƙarfi a yankin da suka haɗa da Turkiyya, lran, Saudiyya, Qatar da lsra'ila sun mayar da Siriyar wajen gwada matsayin su.     

Akan wannan sabuwar maudu'in mun sake kasancewa tare da malam Yazar Can ACUN daga cibiyar nazarin ilimin Siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Turkiyya.

A cewar sa:

Ƙasashe masu ƙarfi a duniya dama na yankunan Siriya sun kafa wakilai domin cimma burinsu a ƙasar Siriya. Da farko dai ƙasar Rasha da haɗin gwiwar lran sun kasance masu baiwa gwamnatin Asad gudunmawa musamman na kuɗi da horar da sojojin ƙasa da sama a Siriyar. Bayan haka lran ta kasance tana baiwa gwamnatin Asad tallafin kuɗi dana soja, a yayinda take kuma kafa wasu kungiyoyin da ke goyon bayan gwamnatin Asad din a Siriya. Ire-iren waɗannan kungiyoyin sun haɗa da  Hizbullah din Lebanon, Fatimiyyun Tugayı din Afganistan, Nujeba din Iraqi da kuma Zeynebiyyun ɗin Pakistan sun kasance wakilan kasashen waje a Siriya. Bayan wakilan lran a kasar Siriya akwai kuma wadansu kungiyoyin dake gudanar da ayyukan kare al'umma a kasar. Wakilan lran a Siriya basu kasance ba facce kungiyoyin dake yunkurin kare manufofin lran a Siriyar. Sojojin lran da Rasha sun kafe sansanoni a kasar Siriya har ma a filayen tashi da saukar jiragen saman kasar.

Waɗansu kungiyoyin kuma su ne waɗanda Amurka, Faransa da lngila suka kirkira. Ƙasashen yamma dake sunan yaƙi da DEASH sun karfafa kungiyar ta'addar PYG a kasar. Yankunan Arewa maso yammacin Siriya da suka haɗa tun daga Membich har zuwa kudu maso gabashin Abu Kamal sun kasance ƙarƙashin mamayar kungiyar ta'addar YPG da ƙungiyoyi masu ra'ayi irin nata.

Amurka da Faransa kuwa nada kusan sansanonin soja 25. Biyu daga cikin sansanonin kasashen yammaci na amfani dasu a matsayin filin tashi da saukar jiragensu. Bugu da kari, a yankin Tenef dake kudancin Siriya Amurka da lngila nada sansanoni biyu a yankin. A wannan yankin suna gudanar da atasayen da ake kira Magawir Al Sawra. Duk da Saudiyya ta jima tana baiwa masu adawa da gwamnatin Asad gudunmawa, a ƴan kwanakin nan ta fara baiwa kungiyar demokradiyya da YPG ke jagoranta tallafi. Hakan dai na nuni da kasashen Larabawan da Saudiyya ke jagoranta na neman samun ƙarfi a yankunan da kungiyar demokradiyya ke mamaya.

Hakama ba a bar Turkiyya a baya ba wajen kafa sansani a kasar Siriya, Turkiyya ta kafa sansanoni 9 a yankin ldlib domin samar da yankin lumana. Tana kuma da niyyar kafa sansanonin kula 12. Haka kuma, zata cigaba da ajiye sojojin ƙasarta a yankunan da ta gudanar da hare-haren Firat Kalkanı da reshen zaitun da ta kauda kungiyoyin DEASH da YPG.  A yankunan Afrin, Azez, Al Bab da Jerablus da ta samar da zaman lafiya, sojojin kasar masu zaman kansu na baiwa ƴan sandar Siriya horo domin ci gaba da samar da lumana a yankunan.Ƴan sandar Siriya da ƴan adawar ƙasar ta samar sun kafa gwamnatin wuccin gadi da duniya ta amince da ita.

Ita kuwa Qatar ta kasance tana goyon bayan ƙungiyoyin dake adawa da gwamnatin Siriya kafin afkuwar rikicin yankin gulf, rikicin yankin gulf din dai ya sanya Qatar ja da baya daga lamurkan ƙasar Siriya.

Sai kuma ƙasar Isra'ila, wacce ta mamaye tsaunukan Golan ɗin Siriya a lokacin yaƙin lsra'ila a shekarar 1967 lamarin daya saɓawa dokar ƙasa da ƙasa, ta dauki matakan ƙara mamayar yankin bayan ɓarkewar yaƙin Siriya a shekarar 2011.

Haka zalika, Isra'ila wadda ta kasance cikin zullumin yadda wakiliyar lraƙi wato Hizbullah ke ƙara ƙarfi a Siriya, ta dinga kai hare-hare akan kungiyar Hizbullah din lran da lraqi a Siriyar.

Gwamnatin Asad data ƙi jin koken ƴan ƙasarta a shekarar 2011, ta jefa ƙasar cikin yaƙin basasan da ya maida ƙasar fagen gwajin bajintar manyan ƙasashen duniya da ma na yankunan a kaikaice. Haƙiƙa, Siriya wacce ta rasa ƴancinta kasashe sun tsattsagata inda kowa ya kama nashi barayin. A halin da ake ciki babu ko alamun janyewar manyan ƙasashen duniya dana yankin daga ƙasar, haƙiƙa Siriya ta kasance cikin yaƙin basasa da ke ci gaba har ila yau.

Wannan sharhin Mal Yazar Can ACUN ne manazarci a cibiyar  nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.

Mu huta lafiya….Labarai masu alaka