Turkiyya zata tauna taura biyu lokaci guda

A daidai lokacin da Turkiyya ke ƙoƙarin ɗaukar matakai akan iyakokinta zata kasance kuma cikin yanayin zaɓe, zata dai yi amfani da dan ƙarfin siyasa, soja da tattalin arziki da take dashi domin ƙalubalantar yunkurin Amurka akan canja tsarin yankin.

Turkiyya zata tauna taura biyu lokaci guda

Lamurkan dake faruwa a tsakiyar ƙasashen lraqi da Siriya na ƙara daɗa nauyi akan ƙasar Turkiyya, a cikin irin wannan halin ne kuma Turkiyya zata gudanar da zaben shugaban kasa. Matsalolin cikin gida dana iyakoki suna daga cikin dalilan da suka sanya yanke hukuncin gudanar da zaben shugaban ƙasar Turkiyya da wuri da za'a yi a ranar 24 ga watan Yuni. A daidai lokacin da Turkiyya ke ƙoƙarin ɗaukar matakai akan iyakokinta zata kasance kuma cikin yanayin zaɓe, zata dai yi amfani da dan ƙarfin siyasa, soja da tattalin arziki da take dashi domin ƙalubalantar yunkurin Amurka akan canja tsarin yankin, zaɓen da za'a gudanar a ranar 24 ga watan Yuni matakin farko ne akan hakan.          

Akan wannan sabuwar maudu'in mun sake kasancewa tare da Mal Yazar Can ACUN dake Cibiyar siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Turkiyya.

Kasancewar yadda lamurkan kasar Siriya da lraqi har yanzu basu daidaita ba, Akwai buƙatar Turkiyya ta kara ɗaukar matakai a iyakokinta, musamman  a kudancin ƙasar.

Kafa sabuwar gwamnati ba zai dauki Turkiyya watanni shida kaman wadansu Ƙasashen Turai ba. Turkiyya dai na bukatar daukar kwararan matakai akan yadda lamurka suka kasa daidaita a gabas ta tsakiya. Zaɓen da za'a gudanar a ranar 24 ga watan Yuni zai baiwa Turkiyya ƙwarin gwiwar ɗaukar matakan da suka dace a yankunan. Duk da dai ana da ƙarancin lokaci na watanni biyu kafin gudanar da zaɓen wannan matakin ka iya canja lamurkan yankin kasancewar yadda Turkiyya zata maida hankali akan lamurkan zaɓe a ƙasar. Duk da haka zaɓen ka iya kange yunkurin sake sauya tsarin ƙasar Siriya.

Kasancewar yadda Amurka keta hurɗa da barayin ƙungiyar ta'addar PKK a Siriya wato YPG da kuma yadda lran da Rasha suka hada gwiwa da gwamnatin Asad da kuma yadda lsra'ila ke ƙara gwamatsan yankin, Turkiyya ta tilastu da ɗaukar matakai domin ƙare ƴancin ƙasarta.

A daidai lokacin da Turkiyya, Rasha da lran keta kokarin samar da lumana a Siriyan bisa tsarin yarjejeniyar Astana, Amurka da kungiyar YPG na gudanar da wadansu ayyukan daban. Yunkurin da Amurka keyi na horar da mambobin ƙungiyar ta'addar YPG dubu 65 a ƙarshen shekarar 2018 zai kawo cikas ga yancin kasar Siriya da kuma haifar da ƙalubalolin tsaro ga Turkiyya

Ƙasashen duniya da sauran ƙungiyoyi sun fara nuna irin matakan da zasu ɗauka bayan kauda ƴan ta'adda a Siriyan, hakan ya biyo bayan kauda dukkan ƴan ta'addar Siriya baya ga kungiyoyin DAESH da YPG. Duk da hakan ka iya daukar shekaru, bayan kauda ƴan ta'addar kasar inda Siriya ta dosa zai bayyana. Akwai bukatar Turkiyya da ta kasance makwabciyar Siriya mai muhimmanci, ta dauki matakai akan lamurkan yankin koda yaushe.Turkiyya ta bayyana aniyar gudanar da  wannan zaɓen domin ta samu damar ɗaukar matakan da suka dace ƙwarara a yankin.

Haka kuma kasancewar Ƙungiyar PKK a yankin lraqi da suke ƙalubalantar Turkiyya, ya sanyata ɗaukar matakan soja domin ƙalubalantar ta'addanci a yankin. Sai dai zaɓen da ake shirin gudanarwa a lraqi zai kawo cikas ga yaƙar ta'addanci a kasar, amma idan aka kafa gwamnati a lraqi  Turkiyya zata haɗa gwiwa da sabuwar gwamnatin domin ƙarar da kungiyar PKK a yankin.

Kungiyar ta'addar PKK dai ta mayar da tsaunukan Kandil da tsaunukan Sincar tushenta. Gudanar da zaben ƙasar Turkiyya da ake shirin yi da wuri zai kara bada ƙwarin gwiwar daukar matakai kwarara domin ƙalubalantar ƙungiyar ta'addar PKK a Siriya.

A hakikanin gaskiya, sabuwar tsarin mulkin shugaban kasa da za'a aiyanar bayan zaɓe zai kauda ka'idodi marasa kan gado da kan haifar da cikas da jinkirin gudanar da lamurka a kasar. Turkiyya zata ƙara karfafa a fannonin siyasa da tattalin arziki bayan sauya tsarin jamhuriya zuwa na shugaban ƙasa a ƴan watannin dake tafe, lamarin da zai bata damar ɗaukar matakan da suka dace a yankunanta baki ɗaya.

Wannan sharhin mal Yazar Can ACUN ne daga cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.Labarai masu alaka