Babban zaben Turkiyya na 32 kuma na shugaban kasa na farko

Za mu kalli wannan batu tare da sharihin da Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana wanda shi ne Shugaban Tsangayar Nazarin Kasa da Kasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

Babban zaben Turkiyya na 32 kuma na shugaban kasa na farko

A ranar 24 ga watan Yuni Turkiyya za ta gudanar da zaben shugaban kasa. A tarihi wannan ne karo na 32 da za ta yi babban zabe kuma karo na farko da za ta yi zaben shugaban kasa.

A lokacin Daular Usmaniyya aka fara zabe na farko na gama gari a Turkiyya a shekarar 1876. Daga baya kuma aka yi zabukan shekarun 1878, 1908, 1912, 1914 da 1919. An yi zabuka sau 6 a wannan lokaci. A lokacin jamhuriya kuma da ake da jam’iyya 1 an yi zabuka sau 25. A lokacin jam’iyya 1 an yi zabuka a shekarun 1923, 1927, 1931, 1935, 1939 da 1943 wato sau 6 kenan. Daga shekarar 1946 da aka fara amfani da jam’iyyu da yawa kuma an yi zabukan gama gari sau 19. Zaben 24 ga Yuni ne zai zama zabe na 20.

Tun daga shekarar 1876 da aka yi zabe na farko a Turkiyya, har zuwa 24 ga watan Yuni da za a yi zaben shugaban kasa, an gudanar da zabuka na gama gari sau 32. A gefe guda kuma akwai lokuta da ba a yi zabe ba saboda juyin mulkin da aka gudanar.

Lokutan zabe daban-daban

Babu tantama ko shakku, kowanne zabe ko kuma lokacin zabe na da abubuwansa masu kyau. Zabukan da aka yi a lokacin Daular Usmaniyya, zabuka ne da aka yi su a lokacin da ake da tsari na Sarki, Mai gari, Shugaban Addini da Halifanci. Saboda Turkiyya kasa ce da ta kasance karkashin Daular Musulunci da Tsarin Shugaban Musulmi da Halifanci ya sanya babu wata muhawara sosai game da ko Musulunci da Demokradiyya za su tafi tare ba.

A tsakanin 1923 da 1943 an gudanar da zabuka karkashn jam’iyya 1 kawai. Yana da ma’ana matuka duk da cewa, ba a ba wa ‘yan adawa dama a zabe, amma an ci gaba da zabukan kuma lokaci ne da ba a manta da al’adun baya na Daular Usmaniyya ba inda aka kuma kauce wa tsarin nuna wariya da kyamar yahudawa na Yammacin Duniya.

A shekarar 1946 Turkiyya ta samu jam’iyyun siyasa da yawa. A tsakanin 1876 da 1946 an yi dabuka masu matakai 2, amma zabukan da aka yi daga 1946 zuwa yau suna da mataki 1 ne. Tsarin daraja biyu shine tsarin da ke kama da na Amurka a yau. A wannan tsarin masu zaben ne suke zabar ‘yan majalisa. Zabe mai daraja biyu na samar da rashin tsaron kuri’u.

A ranar 24 ga watan Yuni Turkiyya za ta yi zaben shugaban kasa a karon farko. Tun daga 1876 wannan ne karo na farko da za a yi zaben shugaban kasa da zai kafa gwamnati da na ‘yan majalisa daban-daban. A rubutun da na yi a 2017 mai taken “Tsarin Shugaban kasa don smaun Turkiyya Mai Karfi da Zaman lafiya” na yi bayanin bukatar da ta sa ake son tsarin Shugaban Kasa wajen gudanarwa a Turkiyya.

Ma’anar zabukan

Demokradiyya ba tana samun karfi daga abinda ta kunsa ba ne, tana samu ne daga damar da ta bayar. A baya hanyoyin samun iko na demokradiyya na da bambanci. A nan gaba ma wasu hanyoyin ne za su zo. Amma a yau, watakila hanya ta musamman ce ke ba wa al’uma cikakkiyar dama da karfin iko. Sakamakon haka ta hanyar zabe, ne ya ke da muhimmanci a samar da gwamnati da masu shugabancin jama’a tare da ba su karfin iko. Gwamnatotin da suka sam iko ta hanyar zaben sun fi samun karfi a kasarsu da ma kasashen waje. Al’umun da suke samun karfi ba ta hanyar siyasa ba kuma ba sa samun karfi. Ana samun zalunci, take hakkokin dan adam da danne ‘yanci a irin wadannan gwamnatoci,  kuma suna zama marasa karfi a wajen saboda ba su samu iko da karfi daga jama’arsu ba. Saboda haka sai su koma neman goyon baya tare da dogara ga manyan lkasashen duniya.

Idan aka kalli cigaban demokradiyya, za a ga yadda al’umun da suka rungumi tsari na siyasa da demokradiyya suke zaune kalau. Yau a duniya kasashen da suka fi cigaba tare da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kasashen enda suka rungumi demokradiyya. Kasashen da suke cikin matsala kuma su ne wadanda suka yi watsi da demokradiyyar. Idana ka kalli wannan abu za a ga cewa, ashe karfin da dorewar demoktadiyya ne karfin kasa da ma na tattalina arzikinta. A duk inda babu zaman lafiya to babu cigaba.

Daya daga cikin babban m,isali da za mu iya bayarwa game da cigaba, ‘yanci, zaman lafiya da kwanciyar hankalida demokradiyya shi ne irin matakan da Turkiyya ta dauka bayan shekarar 2000. Bayan juyin mulkin 28 ga watan Fabrairu tare da fuskantar abubuwa da suke rushe demokradiyya, kudin da kowane dan Turkiyya ke samu a shekarar ya sauka zuwa dala dubu 2000. Amma bayan shekarun 2000, a lokacinda aka samar da tsari na ‘yanci da walwala, sai wannan kudi ya kai har dala dubu 10.

Idan aka yi tunani game da zaben farko da Turkiyya ta yi a shekarar 1876, to tarihin siyasar Turkiyya ya fi na kasashe da dama dadewa. A wannan lokaci na shekaru 142 duk da an samu gwamnatoci daban-daban amma Turkiyya ta ci gaba da aiwatar da demokradiyyarta. Idan aka waiwaya baya, idan aka kalli aiyukan adawa da demokradiyya, Turiyya ba ta zama kamar Jamus da Italiya ba da suka fuskanci zamanunnukan kyama da adawa da Yahudawa. Bayan shekarun 2000 demokradiyya da ‘yanci sun samu daukaka da kankama a Turkiyya. An bar tsari kama karya da cusgunawa. Ko kasashen Jamus, Holan da Ostiriya da suke take hakkokin Tuırkawa da ke kasashensu wajen hana su zabe, to hakan na sake nuna wa duniya yadda Turkiyya ta ci gaba wajen dabbaka demokradiyya. Masu zako, za su iya bin diddigin zaben da za a yi a Turkiyya wanda na iya zama mafi kyau a duniya saboda kasa ce da ta dauki shekaru 142 tana zabuka karkashin doka da shari’a kuma cikin tsaro.

Mun kawo muku Sharihin da Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana wanda shi ne Shugaban Tsangayar Nazarin Kasa da Kasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara ya yi mana...Labarai masu alaka