Tsaron Isra’ila ne? Ko kuma Mamaya da Fadadarta?

A kan wannan batu za mukawo muku Sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazit Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana.

Tsaron Isra’ila ne? Ko kuma Mamaya da Fadadarta?

Matsalolin Kasashen Duniya: 16

Ta hanyar zababbun kalamai suna bayani. Batutuwan da kuka kalla ta mahangar da kuka so ne zai bayyana matsalar da kuma yadda za ku iya magance ta.

Bari mu bayar da misali da za a iya fahimtar sa sosai batun “Musulunci Mai Sauki” abu ne da za ku iya dauka ku yi amfani da shi. Asali abunda kuke ganin yana da matsala shi ne Musulunci. Idan kuna tattaunawa kan wannan batu to kuna amfani da munanan kalomomi irin su “tsauri, sauyin tunani, masu jihadi, tsattsauran ra’ayin Musulunci amma kuma mafi dama-dama shi ne Musulunci Mai sauki.”. kamar yaddda na rubuta a baya, idan kuka dauki “Yamma mai sauki”, to za ku duba irin cutarwa da zaluncin da kasashen yamma suka yi wa mutanen duniya, a lokacin da yamma ta zama mai saukin ra’ayi za ku nuna irin abubuwan da suka mikawa mutane ko za su gabatar musu.

Abubuwa 2 ne suke daukar hankali kan nazari game da gabas ta tsakiya musamman ma rikicin Siriya. Na farko shi ne ana yin nazari kan Gabas ta Tsaliya kamar babu wata kasa da ake kira Isra’ila. Kamar yadda ya ke a rikicin Siriya, a Gabas ta Tsakiya gaba daya ana mantawa da Isra’ila idan ana nazari da rubutu. In haka ne tun bayan kafa Isra’ila jama’ar Gabas ta Tsakiya suka fada cikin masifu mafiya muni a cikin tarihi. Ana kuma manta wa da tasirin Isra’ila a Siriya. Yin hakan na janyo jama’ar Gabas ta Tsakiya na mika wuya ga manufofin Isra’ila a yankunansu. Tun daga farko zuwa yau, idana ka tambayi kasashen da suka yi rashin nasara a yakin, to za a ga akwai kasashe da yawa. Amma kuma za a ga kasar da ta yi nasara it ace Isra’ila kadai. A lokacin da ake yakin duk wata kasa da Isra’ila ke tunanin tana mata barazana na rasa tushenta da rugujewa. Iran, Turkiyya, kasashen Larabawa na ta rasha tushensu. Baya ga Siriya su ma wadannan kasashe suna asara sosai. Wadansu kasashe da suke kare Falasdinawa a baya a yanzu sun kasance suna kulla kawance da Isra’ila.

A gefe guda kuma, kasashen duniya sun yi shiru tare da kin sukar yadda Isra’ila ke take hakkokin dan dam da kara yada manufofinta, amma sun mayar da hankali kan Siriya kadai.

Abu na 2 da aka rasa a wajen nazarin da ake yi shi ne, tare da mantawa da Isra’ila inda ake mayar da hankali kan Siriya kadai, to hakan na nuna yadda tsaron Isra’ila ya ke. Dukkan masu nazari na Turai da wasu daga Gabas ta Tsakiya na bayar da bayanai da cewa, “Tsaron Isra’ila”. Idan aka kalli matsalar daga bangaren tsaron Isra’ila, to ana halarta irin barna da tabargazar da Isra’ila ta aikata zuwa yau ne a Gabas ta Tsakiya. A tsari na gaskiya shi ne kowacce kasa za ta tashi ta tsare kanta daga duk wata matsala ta tsaro da ta taso mata. A nan idan wata kasa na daukar matakai, to za a iya sukar ta matukar ta take hakkokin dana dam tare da zaluntar wasu mutanen.

In haka ne, to matsalar da aka dauki shekaru 50 ana fuskanta a Gabar ta Tsakiya ba ta tsaron Isra’ila ba ce. Yadda kafafan yada labarai a lokuta daban-daban suke yada taswirar yadda Isra’ila tun 1947 ta ke mamaye yankunan da ta ke, abu ne na nuna gaskiya. A shekarar 1947 Yahudawa na zaune ne a wani dan yanki na kasar Falasdinawa, amma a yau abun ya juya. Taswira na nuna yadda yankunan Falasdinawa suka dawo kadan tare da kare wa. Suna zaune a waje kamar kurkuku. Dan jarida Mehmet Akif Ersoy da ya tambayi wani matashin Bafalasdine cewa, “meye burinka” sai ya ce, irin na bakin cikin yadda aka mayar da kasarsu kamar kurkuku. Wato shi ne “Yin tafiya da mota ta kilomita 180 ba tare da samun cikas daga Isra’ila ba.”

A gefe guda, babu tabbas din Isra’ila za ta ci gaba da mallakar yankunan da ta mamaye. Duk da cewa, wasu yahudawa na adawa da hakan, ba abu ne boyayye ba wada wasu yahudawan suke bin asalinmanufar da aka kafa su a kai. Bincike ta yanar gizo kadai zai iya nuna yadda wannan abu ya ke karara. A karkashin manufar Isra’ila mai girma, Yahudawan Zionist suna ikirarin cewa, za su ci gaba da mamaya har sai sun dangana ga tafkin Firat zuwa ga yankunan Kuradawa, Larabawa da ma na wasu Turkawa wanda yankuna ne da aka yi musu alkawari. A yau idan aka kalli rikicin Siriya, to wadannan Yahudawa da inda suke rayuwa ne musabbanin janyo rikicin.

Idan aka kalli manufofin Isra’ila daga lokacin da aka kafa ta zuwa yau, ko kuma idan aka kalli manufofinta a yankunanta, to za a ga Isra’ila na da manufofi na kai hare-hare. Batun da ake na tsaron Isra’ila, to za a ga yadda a boye ta ke kara yaduwa da mamayar yankunanta a siyasance. Saboda haka abinda za a ce karar shi ne Yaduwar Isra’ila ba Tsaron Isra’ila ba.

Mun kawo muku Sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazit Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana.Labarai masu alaka