Halin da Musulman Arakan ke ciki

Jama'a barkanu dai da kuma kasancewa a cikin sabon shirin…. Daga nan TRT hausa Muryar Turkiyya.

Halin da Musulman Arakan ke ciki

Watakila nan da wani lokaci mai zuwa yaronku bai ji cewa, bayan ranar 25 ga watan Agustan 2017 Musulman Arakan ko Rohgya sun guje wa zaluncin gwamnatin Myammar inda sama da mutum dubu 500 suka yi kaura zuwa Bangaladash tare da neman mafaka, wanda haka ya kara ta’azzara mummunan halin da suke ciki.

A wannan makon za mu kawo muku sharhin Shugaban Tsangayar nazarin Siyasa na Jami’ar Yildirim beyazit da ke Ankara Farfesa Kudret Bulbul.

Idan muna son mu san ina Arakan ta ke watakila muna bukatar mu kalli batun ta fuskar taswirar duniya. Arakan jiha 1 ce daga cikin jihohin Myammar 7. Myammar kasa ce da ta ke da iyaka da kasashen Tailan, Laos, China, Indiya, Bangaladash da gabar tekun Bengal. Arakan na da matukar muhimmanci a yankunan da ke gabar teku a Myammar.  

Ana bayyana cewa, Musulunci ya je Arakan ne bayan da wani jirgin ruwan ‘yan kasuwa ya kife kuma aka kubutar da shi a gabar tekun Bengal. Musulman Arakan kamar na Moro sun dade suna rayuwa a karkashin sarakunansu. A shekarar 1885 ne ‘Yan mülkin mallak ana Birtaniya suka mamayi kasar Arakan. Idan har ku ka fa  wasu kifaye 2 da ke fada a cikin teku, to tabbas Ingilawa sun wuce ta wannan wajen”.  Tuna wannan kalamin a tekun Red Sea, bayan Myammar ta samu ‘yanci a shekarar 1948 duk matsalolinta sai suka sake munana. A shekarar 1962 an yi juyin mülki a kasar inda NE Win ya hau kan mülki. A lokcin ne aka canhja sunan kasar daga Burma zuwa Myammar. A lokacin da ake mülkin jamhuriya da jam’iyya daya kasar ta yidukkan mai yiwuwa wajen kakkabe Musulmai. Bai kamata a amanta da hare-haren mabiya Addinin Budha masu sunan ‘yan gwagwarmayar 969 da suke ta kashe Musulmai.

Idan mukakalli halin da Musulman Arakan suka tsinci kansu a ciki sai mu ce babu abin za mu gani sai bakin ciki da bacin rai, hawaye, gudun hijira, da zubar da jini.

Domin bayyana matsalar da Musulman Arakan suke ciki mun taba shirya wani taro inda muka gayyaci Shugaban majalisa Al’umar rohingya na nahiyar Turai da kuma mataimakin babban sakatare a ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya zuwa jami’ar yildirim beyazit.

Bakonmu da ya zo daga kasar Holan yana amfani da sunaye 2. La jo da Muhammad Hubayb. Da muka tambaye shi dalili sai ya ce, sai ya bayar da amsa a hukumance. A myammar domin guje wa zalunci kowa ba ya amfani da sunansa na gaskiya. Mu mun san irin wanna abu inda a shekarun 1980 Bulgeriya ta yi wa Turkawa inda ta kai ga kasar kabar ima sai an sauya mata launi.

Tabbas lamarin babba ne, akwa matsala mai girma, amma matukar muna numfasawa to akwai sauran dama kenan.

Abu na farko da za mu ce ana bukatar yi shi ne, kasashen duniya su yi amfani da karfi wajen magance kasar Myammar. İdan har ana maganar take hakki da zalunci, da rashin adalci, to dole ne a yi maganinsa da karfin tuwo. Ya zama lallai kasashen duniya su yi amfani da karfi wajen kawo karshen zaluncin da ake yi wa Musulman Arakan na Mymmar.

Kamar yadda kasashen duniya suka kafa kungiyar magance rikicin yankin MINSK na Yukren hak aza su yi kan Myammar. Mun san cewa, ındiya da China ba wai suna can ba ne don warware matsalar, a a su wani bangare ne nata. Amma duk da hak aza a iya neman hanyar warware matsalar ta hanyar amfani da su. Wannan mataki da za a dauka zai tabbatar da an dawo da jama’ar Arakan kasarsu tare mayar da su gidajensu da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.

Dole ne a maysar da matsalar Arakan ta kasa da kasa. Kamar Kurdawan Siriya, har yanzu Musulman Arakan ba su da shaidar zama ‘yan kasar Myammar. Idan ba su samu shaidar a hukuance ba babu yadda za a yi su samu ilimi, kula da lafiya da sauran abubuwan more rayuwa. Dukkan kungiyoyin s kain a kasa da kasa da na kare hakkokin dan dama za su iya daukar wannan matsala tare da yaya ta ta. Za a iya fara daukar matakai na shari’a. Karar da za a kai gwamnati ko sojojin Myammar kan take hakkokin Musulman Arakan za ta taimaka wajen samun sakamako mai kyau.

Dole a taimaka wa bangaladash. Da ma kasar Bangaladash na cikinmawyacin hali, a yanzu ka zo ka ce mata ta taimaka wa dubunnan daruruwan mutane ka san akwai aiki, a saboda haka bai kamata a kyale ta ita kadai ba.

Dole a ba wa kungiyoyi manya fifiko. Kamar a irinnsu AFAD, TIKA, IHH, Red Crescent da sauran kungiyoyin fararen hula suna taimakawa sosai. Amma kuma idan aka dubi halin matsi da ake ciki ba zai yiwu a mayar da hankali kan taimaka wa mutane kawai ba. Dole a samar da cibiyoyin kawo tsare-tsare da su ma za su bayar da gudunmowa.

Haka zalika dole a samar da wata kungiya ta warware rikici wadda Turkiyya za ta ding aba wa shawara da nusarwa.

Kamar yadda matsalar kudus ba ta shafi Musulmai kawai bai, hak ama matsalar Musulman Arakanta ke, ta shafi kowanne bangare na duniya. Yana da matukar muhimmanci a samar da tsari a matakin kasa da kasa. Ziyarar da Mai dakin shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan Amina Erdoğan ta kain a da matukar muhimmanci.

A wasu lokutan abu daya kan canja, a wasu lokutan kuma abubuwa da yawa ne suke canjawa. Yanayi na sauyawa, tekun Mediterrenean ma haka kamar yadda mai waka ya ke fada. Yauwa kar mu tsaya. Mu taya ‘Yan uwa bacin rai. Yaran Arakan na da makoma mai kyau a saboda haka dole a saka musu ran samun nasara

Mai Sharhi: Farfesa Dakta Kudret Bulbul. Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin kasa da kasa a jami'ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.Labarai masu alaka