Tarihin yankin Troy na Turkiyya

Masoya gidan rediyon muryar Turkiyya, barkanmu da sake saduwa damu a cikin wani sabon shirinmu na Tarihin yankin Anatoliya tare da ni ADAM ABUL-BASHAR. A cikin shirinmu na wannan mako, zamu dora daga inda muka saya a cikin shirinmu na makon  da ta gabata.

Tarihin yankin Troy na Turkiyya

Idan baku manta ba, a cikin shirin mu na makon da ya gabata mun yi muku alkawarin cewa zamu baku labarin yadda yakin Troy ya kasance. Dan sarkin Troy wato yarima Paris ya zabi ‘yar Atina Helen a matsayi mace mafi kyau a cikin farkon gasar kyau da aka gudanar na tarihi inda Paris ya sace Helen ya gudu da ita. Maganar gaskiya shi ne yarimar Troy Paris ya sace Helen matar  sarkin Atina Menelaos na tsawon shekaru 10 inda a dare daya, sai Paris ya saceta. A lokacin da aka sace matarsa sai sarkin Atina ya fusata inda ya yada labarin a garuruwan garin Girka baki daya. Bayan haka sai ya tattara soji masu yawa. Inda wadannan sojoji suka shirya domin su je farautar kama wanda ya sace matar.  Tarihi ya nuna cewa wannan tashin hankali da aka yi a cikin shekarar 2200 kafin miladiyya ya zama sanadiyyar da mutanen Troy suka koma da zaya a gabar tekun Çanakkale da ke Asiya. Shi ya sa  wadannan sojoji da suka dauki hanya cewa zasu yaki mutanen Troy, sai suka kasa nasara. An dauki tsawon shekaru 10 mutanen Girka na neman hanyar da zasu yaki mutanen Troy wanda hakan ya haifarmusu da rashin kwanciyar hankali. A wannan lokaci ne sai sojojin suka fara daga muryar cewa suna son su koma gidajensu da garuruwansu. A wannan lokaci kuma sai sarkin Atina Menelaos ya kasa neman mafitar abin da ya kamata yayi. Da ya kama shawara da manyan mutanensa, sai suka bayyana mishi cewa ba zai iya yin nasarar yakin amma sai dai zai iya yin nasarar akansu ta hanyar yaudara. A cikin mutanen da suka bishi suka tafi yakin, ciki harda jarumi Akhilleus. Bayan haka kuma akwai dan sarkin wato Hektor wanda tarihi ya nuna cewa jarumi ne. Ko da yake ya san cewa zai mutu a wurin yaki ceto Helen amma sai da ya daure ya tafi. Ya yarda cewa za a harbeshi ya mutu saboda tun da yake yaro mahaifiyarsa mata shayardashi ba ta gudu ta barshi. A yayin da ake yakin Troy, sai Paris ya harbeshi da kibiya inda ya kashe shi. A yau mutane sun yarda cewa yankin Aşil Tendomu a wurin ne aka harbeshi.

Sarkin Atina yayi kokari inda ya binciko hanyar yaudarar da zai bi domin yin nasarar yakin inda sai daya daga cikin kananan sarakansa Odyseus  ya bashi shawarar cewa, ya bar a kera masa dokin itace sai ya bar sojinsa su shiga ciki bayan haka sai ya sanarda cewa ya ja baya daga yakin da ake yi. Wannan shawara ya bayar sai Menelos ya yaba. İnda ya bar aka yi kamar yadda karamin sarkin ya bada shawara, bayan da sojin sun shiga cikin dokin sai ya sanarda cewa ya ja baya daga yakin da ake yi. A gefe guda kuma sai mutanen Troy suka yi murnar cewa makiyansu sun janyae daga yakin kuma sun bar yankin. Amma sai suka ga cewa akwai babban itace a filin dagar. Sai mai bokar cikinsu ya ce musu idan suka dauki wannan itace zai zama wani bala’i a garesu. Amma sai kash, basu saurareshi sa suka dauki itacen suka kawo a wurin ibadarsu. Tsakar dare a lokacin da mutanen Troy suka yi bacci a buge domin murnar cewa sun yi nasarar yaki sai Odyseus da sojinsa suka fito suka mamaye garin baki daya. Binciken da masu tone-tone suka yi na nuna cewa a cikin shekarar 2200 kafin miladiyya an kona gari. Kuma an kona wanna gari ne karkashin jagorancin sarkin Atina.

A yau mutane sun samu cikakken labarin yakin Troy ne bisa littafin İlyada ve Odyesseia da dan garin Bodrum Homeros ya rubuta. A cikin karni na 19 kuma sai Schlimann  ya kamu samu labarin littafin da matarsa ta karanta inda sai ya zo yankin Çanakkale ya gano garin Troy tare da yin tone-tone domin binciko kayayyakin tarihi. Sanadiyyar binciken da yayi ya bar duniya baki daya ta gano cewa ba wai tasuniya suka karanta ba shekara da shekaru, domin a gaske al’amarin ya faru. A yau akwai dokin Troy na al’ada da ke bada labarin al’amurran da suka faru. Kuma a yau mutane da anfani da karin magana a lokacin da kwamfuta ya samu matsala da cewa ciwon Troy ya kamata.

 

 Labarai masu alaka