Gwagwarmayar Gabas ta tsakiya a yau

Bayan kwasan mutane da aka yi a Aleppo, yawancin ‘yan adawa Turkmen sun fita daga garin Idlib karkashin jagorancin dakarun Free-Syrian Army inda suka shiga cikin yakin Tsaron Fırat.

Gwagwarmayar Gabas ta tsakiya a yau

Shi ya sa muma muka yanke shawarar cewa a cikin shirinmu na wannan mako zamu tattauna al’amurran da suka faru a lokacin da ake kwasan mutane daga Aleppo, halin da al’ummar Turkmen ke ciki a Siriya da kuma samun cigaba da ake yi a cikin hare-haren Tsaron Fırat.

        A lokacin da aka shiga shekarar 2017, a kasar Siriya kuma za a shiga cikin sabon lokaci. Shi ya sa bangarorin siyasar kasar Siriya suna sake duban matsayinsu kuma suna sake dubar hanyoyi da zasu bi domin mulki a cikin kasar. Daya da daga cikin mutanen da ke fadi a cikin kasar Siriya kuma su ne al’ummar Turkmen da ke Siriya.

        Bayan kwasan mutane da aka yi a Aleppo, yawancin ‘yan adawa Turkmen sun fita daga garin Idlib karkashin jagorancin dakarun Free-Syrian Army inda suka shiga cikin yakin Tsaron Fırat. An fara wannan hare-haren Tsaron Fırat ne a ranar 24 ga watan Agustan shekarar 2016 inda jami’an tsaron kasar Turkiyya suka taimakawa dakarun Free-Syrian Army da dakarun Turkmen wurin korar kungiyar ta’adda ta Daesh a Jarablus. Jaruman dakarun Turkmen kamar Muntasır Billah, Fatih Sultan Mehmet da Sultan Murat Tümeni na cikin wadanda suka taimaka wurin yaki da Daesh yankinsu na Siriya.

        Da ma al’ummar Turkmen da muke magana akansu suna da hedkwata tsakanin yankin Azez da Jarablus. Al’ummar Turkmen sun dauki tsawon lokaci suna yaki da Daesh domin su kiyaye yankinsu. Wannan shi ne dalilin da ya sa suka taimakawa dakarun Free-Syrian Army wurin kwasan mutane daga Aleppo tare da anfani da hedkwatar da su wurin shiga yakin Al-Bab domin yaki da ‘yan ta’addan. Ba zamu tabbatar muku cewa akwai tsaro a yankin ba amma zamu iya ce muku akwai mutane da dama suka shiga cikin yake-yaken da ake yi.

        Ana maida hankali sosai wurin hare-haren Tsaron Fırat domin ganin cewa mutane basu shiga cikin matsala ba domin ana lokacin tsanyi. Amma halin yanzu abinda zamu iya fadi shi ne, kungiyoyin ta’adda ta Daesh, PKK/YPG dukkaninsu na cikin mawuycin hali. Misali, ya zuwa yanzu jami’an tsaron Turkiyya sun lalata bamabaman hannun na Daesh 2335 tare da bambaman da aka binne karkashin kasa 42. Babu shakka yawancin wadannan bama-bamai da aka samu kasashen Yamma ne suka taimakawa kungiyar Daesh. Bayan dakatar da hare-haren Rakka da Mosul ne sai kasashen yamma suka fara taimakawa kungiyar da ke Al-Bab.

        A halin yanzu, Turkiyya ta kusan kammala hare-haren da take kaiwa Daesh kuma zata hana kungiyar ta’adda ta PKK motsi a gabashin Siriya. Wannan shi ne dalilin da ya sa aka dauki matakin tsaro masu muhimmanci a gabashin kasar Siriya domin a wurin ne akwai garin Bab.

        A Gabshin Siriya ko kuma mu ce Siriya baki daya ana son canje-canje kamar yadda ake so a kasar Siriya. Shi ya sa idan za a yi tunanen wannan yanki, kamata ne a yi tunanen yankin Kudu maso Gabashin Anatoli da kuma arewacin Iraki baki daya. Tarihi ya nuna cewa a lokacin daular Turkiyya, an yi mulkin kudu maso gabashin  Anatolia , arewacin Siriya da kuma arewacin Iraki; a matsayin Diyarbakır, Aleppo da Mosul. 

        A yau akwai kayuka kusan 150 tsakanin garin Azez da Jarablus. Wadannan kauyuka na karkashin ikon al’ummar Turkmne da suka shiga cikin hare-haren Tsaron Fırat. A kudancin yankin da ake kai hare-haren Tsaron Fırat akwai kusan kauyuka 60 na al’ummar Turkmen. A tsakanin Akçakoyunlu da Münbiç, akwai kauyuka sama da 50. A kudancin Munbiç kawai akwai kayuka mutanen Turkmen 15. A yau arewa maso gabashin Aleppo wato cibiyar Çobanbey da Bab akwai kauyukan Turkmen 50. A kudancin Sacur Suyu kuma akwai kauyukan al’ummar Turkmen fin 20. Haka abin ke tafiya shi ya sa akwai wurare da dama a kasar Siriya wanda yake mulkin al’ummar Turkmen ne.

        A cikin ‘yan kwanakinan Daesh na tsoron shiga arewacin Siriya, Jamhuriyar Turkiyya da kuma ‘yan adawa. Idan aka yi nasara har Al-Bab ya fita hannun ‘yan ta’addan, to babu shakka zai zama an yakesu kenan. Ta haka ne dukkan yankin da Daesh ta zata shiga Turkiyya zata iya yakenta kuma haka zai zama wani tashin hankali tsakanin gwamnatin Asad da kungiyar ta’adda ta PKK/YPG.

        Mutanen tunen cewa nan gaba, al’ummar Turkmen da yawa zasu shiga cikin hare-haren Fırat kuma zasu samu ‘yancin magana a kowanne lokacin da za a tattauna maganar da ta shafi kasar. Idan kasashen waje suka bayar da dama, nan gaba al’ummar Turkmen zasu iya taka muhimmiyar rawa a wurin kafa demokradiyya da kuma tsarin raba gwamnati da addini a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Siriya. Idan aka amince da al’ummar Turkmen, zata iya nasara wurin yaki da dukkan kungiyoyi masu anfani da makamai. Ta haka kuma kasashen Turai zata iya kare kanta daga masu neman mafaka, salafiyya, masu anfnai da makamai da kuma kungiyoyin ta’adda dake kai hare-hare da sunar suna jihadi.

 



Labarai masu alaka