Rana Irin ta Yau 04.02.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 04 ga watan Fabrairu.

Rana Irin ta Yau 04.02.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 04 ga watan Fabrairu.

Ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 1783 ne Amurka ta kawo karshe yankin neman 'yancin cin gashin kai da ta fafata da Masarautar Burtaniya  tare da ayyana kiyayyar da ke tsakanin ta da Ingila har illa mashallah.

Ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 1789 ne aka zabi George Washington a matsayin shugaban kasar Amurka na farko.A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 1792 kuma,ya sake jan ragamar mulki a karo na biyu.

Ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 1794 ne Faransa ta haramta bauta a illahirin kasashen da ta ke ci gaba da reno.Kasar dai ta bi Amurka ta Arewa wanda a karni na 18 ta hana a bautar da mutane.Amma wannan matakin bi jima ba sosai,saboda a shekarar 1802 hawansa kan karagar mulki ke da wuya,sarkin Faransa Napoleon Bonapart ya sake dawo da bauta a duk fadin daularsa.

Ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 1871 ne Sheikh Shamil, hamshakin malamin nan da ya nuna jarumtaka a gwagwarmayar 'yantar da kasar Turkuwan Kafkasiya,ya kwanta dama a kasar Saudiyya inda ya je sauke farali.A lokacin kuruciyarsa,Sheikh Shamil ya taka muhimmiyar rawa wajen kubuto al'umomin Kafkasiya daga mulkin mallakar kasar Rasha.

Ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 1495 ne kasashen Burtaniya da kuma Rasha Soviet a birnin Yalta na Tarayyar Soviet.A karshen wannan taron wanda aka yi shi a lokacin yakin duniya na biyu,an tattauna kan matakan durkusar da Jamus,wadanda suka hada da mamaye ta,kawar da mulkin Nazi da kuma tarwatsa rundunarta.

Ranar ga watan Fabrairun shekarar  1957 ne jirgin ruwa na yaki mai dankare da makaman kare dangi Nautilus na kasar Amurka mai lamba SSN-571 ya yi na wanda marubuci Jules Verne ya ambata a fitaccen littafinsa mai suna "Mil 20,000 karkashin Teku" fintinkau ta hanyar cimma wata tazara mai nisan mil dubu 60,000 ba tare da ya fito fili ba.

Ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 2004 ne daya daga cikin daliban jami'ar Harvad,Mark Zuckerberg  ya kafa kamfanin Facebook.A yau shafin sada zumunta na Facebook ya kasance daya daga cikin shafukan da suka fi samun maziyarta.Labarai masu alaka