Rana Irin ta Yau 28.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 28 ga watan Janairu.

Rana Irin ta Yau 28.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 28 ga watan Janairu.

Ranar 28 ga watan Janairun shekarar 1820 ne aka gano Antartica.An fara yunkurin gano wannan yankin shekaru 300 zuwa 600 gabanin haifuwar annabi Isa Allah ya yarda da shi.A cewar falsafar kabilun Girkawan zamanin dauri,duniya dunkulallen kwallo ne wanda ke kunshe da katafarun sassa biyu madaidaita,daya a kudu daya kuma, a Arewacinsa.Da yake suna da masaniya kan arewacin sashen duniya,sai suka dukufa neman daya sashen.An share karnoni ana neman wannan sashen na kudu na duniyarmu.Duk da cewa akwai kwamandojin jiragen ruwa da dama wadanda suka gane wa idanunsu shimfidar kankara marar iyaka da ta lullube yankin na Antartica,inda kuma suka shata taswirar yankin Antartica kan takarda,amma tawagar masanan kasar Rasha wacce ke karkashin jagorancin Fabian Gottlieb von Bellingshausen da kuma Mikhail Petrovich Lazarev ne,suka fara gano daskararren tekun Antartica.

Ranar 28 ga watan Janairun shekarar 1986, bayan saniyoyi 73 da harba Challenger kumbo na biyu wanda hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA ta harba bayan tauraron dan adam na Columbia, ta fashe a sararin samaniya.Kumbon Challenger ya tashi a ranar Afrilun shekarar 1983,inda daga bisani ya dinka kewaye duniya sau tara gabanin ya fashe.Wannan lamarin ya rutsa da rayukan tawagar mutane 7,wadanda suka hada da kwararru 'yan sama jannati 5 da malamai 2.An sanar da cewar,hatsarin ya afku ne sakamakon yoyon man fetur da aka samu daga injin kumbon Challenger.

Ranar 28 ga watan Janairun shekarar 2012 ne daya daga cikin manyan masu fafutukar kare hakkokin 'ya 'ya mata, Keriman Halis ta kwanta dama.A shekarar 1932 sabuwar Jamhuriyyar Turkiyya ta daura damarar kaddamar da manyan aiyukan cigaban kasa.A daidai wannan lokacin ne aka gudanar da gasar mata mafiya kyau na duniya karo na hudu,inda ta lashe kambin sauraniyar kyau ta duniya.Keriman wacce ta halarci wannan gasar kan umarnin gyatuminta wanda daya daga cikin manyan attajiran wancan zamanin,ta samu damar wakiltar gasar kyau ta kasa da kasa ta International Pageant of Pulchritude wacce aka shirya a kasar Beljiyom.A wannan karon ma,Keriman Halis ce ta sauraniyar sarauniyoyin kyau na duniya,inda ta ciri tuta a matsayin mace mafi kyau ta duniya.Abinda yasa zuciyoyin daukacin al'umar Turkiyya suka cika makil da kaunar Keriman,wacce kawo yanzu sunan matashiyar na ci gaba da kasancewa a kundin tarihin mata mafiya kyau na duk fadin duniya kana mace mafi kyau ta farko ta kasar Turkiyya.Abinda yasa 
 Labarai masu alaka