Rana Irin ta Yau 11.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 11 ga watan Janairu.

Rana Irin ta Yau 11.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 11 ga watan Janairu.

Ranar 11 ga watan Janairun shekarar dari shida da talatin ne Manzon Muhammad Bin Abdallah Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya bude Kaaba na birnin Makkah.Wannan babbar nasara da ya yi ta taimaka haikan wajen yada addinin Musulunci a kusurwowi hudu na duniya.

Ranar 11 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da ashirin da daya (1921) ne aka kawo karshen yankin zango na farko na yankin Kurtuluş,inda sojojin Girka suka ja da baya.Turkiyya ta yi wannan babbar galabarta ta farko sakamakon ingantacciyar rundunar soji da Majalisar dokokin kasar ta samar a washegarin nasarar da ta yi a karawarta ta farko da Girka.

Ranar 11 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da ashirin da biyu (1922) ne,aka fara gwada sinadirin insulin a matsayin maganin ciwon suga.Mutum na farko a aka fara maganin a kansa shi ne wani matashi mai suna Leonard Thompsoh mai shekaru  14.

Raran 11 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da arba',in da shida (1946) ne,ya ayyana Albaniya a matsayin kasa mai cin gashin kanta,inda ya zama shugaban na farko na wannan sabuwar kasar.

Ranar 11 ga watan Janairun shekarar alif dari shida da tasa'in da uku (1963) ne, Dutse mai aman wuta na Etna ya fara bore.Tsaunin Etna mai tsawon mita dubu 3,300 ya kasance daya daga cikin duwatsun masu aman wuta mafi girma da kuma tsufa a doron duniya.
 Labarai masu alaka