Rana Irin ta Yau 09.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 9 ga watan Janairu.

Rana Irin ta Yau 09.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 9 ga watan Janairu.

Ranar 9 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da sha shida (1916) ne yakin Seddülbahir,ya suka zo karshe.Seddülbahir ya kasance a jerin manya-manyan yake-yake na karshe wadanda aka fata bayan yakin Çanakkale.

Ranar 9 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da talatin da shida (1936) ne aka kaddamar bikin fara horas da dalibai a tsangayar ilimin adabi,tarihi da na yanayi a jami'ar Ankara a karkashin sa-idon tsohon shugaban kasar Turkiyya,Marigayi Mustafa Kemal Atatürk.Yayin wani bayani da yayi a albarkacin wannan bikin, ministan ilimi na kasar Turkiyya na wancan zamanin,Saffet Arıkan ya ce: "Zamu sake farfado da wayewar duniya wacce a yanzu ake ganin cewa ta gushe".

Ranar 9 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da hamsin da daya (1951) ne aka bude kofofin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya.Duk da cewar cibiyar Majalisar na a birnin New York na aksar Amurka,ana yi wa illahirin yankuna da kuma dokokin da take amfani su a matsayin na kasa da kasa.

Ranar 9 ga watan Janairun shekarar alif da dari tara (1900) ne aka kammala aiyukan layin dogo na birnin Al Kahiran kasar Masar,kana jirgin kasa na farko ya fara da gudanar da zirga-zirga.

Ranar 9 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da tasa'in da daya (1991) ne aka hamrata shan taba sigari a motocin sufuri na bai daya da kuma dakatar da tallace-tallacen duk wasu sinadiran da ke illata kwakwalwar dan adam.
 Labarai masu alaka