Rana Irin ta Yau 07.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 7 ga watan Janairu.

Rana Irin ta Yau 07.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 7 ga watan Janairu.

A ranar 7 ga watan Janairun alif dari shida goma (1610) hamshakin masanin ilimin sirrin samaniya na kasar Italiya,Galileo Galilei ya gano taurari uku da ke kewaye da duniyar Jupiter.An bai wa wadannan taurarin sunayen Lo, Europa da kuma Ganymede,wadanda dukannin su sunaye ne na wasu ababen bauta na tsohuwar Daular Girka.

A ranar 7 ga watan Janairun shekarar alif dari bakwai da tamanin da tara (1789) ne, a karo na farko a gudanar da zaben shugaban kasar Amurka,inda Amurkawa suka zabi wakilai,wadanda su kuma suka zabi George Washington a matsayin shugaban kasar Amurka na farko.

Ranar 7 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da ashirin da bakwai (1927) ne aka fara gudanar ganawar farko ta wayar tarho tsakanin manyen biranen New York da na Landan.

Ranar 7 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da arba'in da shida ne aka kafa jam'iyyar Democrat a kasar Turkiyya.Jelal Bayar, Adnan  Menderes, Fuad Köprülü da Refik Koraltan, wadanda suka juya wa jam'iyyar CHP baya ne suka kafa ta.

Ranar 7 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da hamsin da uku (1953) ne shugaban  Amurka Harry Truman ya sanar wa duniya cewa, kasarsa ta tanadi makamin kare dangi wanda aka kira da iskar Hydrogen.

A ranar 7 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da araba'in da shida (1946) ne,aka fara amfani da na'ura mai kwakwalwa a kasar Amurka.kwakwalwar wannan kwamfutar wacce samfurin "Eniac" ce, na da kaifi sosai.Kamfanin da ya kera wannan na'urara ya taka muhimmiyar rawa a wajen na'urarorin latroni har ya zuwa shekarar alif dari tara da hamsin da biyar (1955).
 Labarai masu alaka