Rana Irin ta Yau 06.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 6 ga watan Janairu.

Rana Irin ta Yau 06.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 6 ga watan Janairu.

A ranar 6 ga watan Janairun 1838 ne Samuel Morse ya gabatrwa da duniya fasahar telegraf da muke amfanida ita wajen sadarwa a yau.

A ranar 6 ga watan Janairun 1921 aka fara yakin Inonu na farko. Turkawa ne suka fara yunkurin korar abokan gaba da suka mamaye yankunansu. A karshe Turkawa sun sami nasarar wannan yaki.

A ranar 6 ga watan Janairun 1956 Turkiyya ta yi nasarar lashe gasar wasa da jiragen sama da kasashe 14 suka halarta a kasar Kanada.

A ranar 6 ga watan Janairun 1960 ne aka assasa tushen gina matatar man fetur ta Mersin. Matatar na tace danyen mai tan dubu 9 a kowacce rana kuma an gina ta da bakin karfe mai yawan tan dubu 15.

A ranar 6 ga watan Janairun 1984 ne aka hana saya da sayar da kudaden kasar waje a Turkiyya amma a yau ana yin haka cikin ‘yanci.Labarai masu alaka