Wani abu ya fashe tare da kashe mutum 1 a Swidin

Mutum daya ya rasa ransa sakamakon fashewar wani abu a wani gida a birn Stolkhom na kasar Swidin.

Wani abu ya fashe tare da kashe mutum 1 a Swidin

Mutum daya ya rasa ransa sakamakon fashewar wani abu a wani gida a birn Stolkhom na kasar Swidin.

Jaridar Aftonbaldet ta bayyana cewa, mutumin mai shekaru 20 ya rasu a lamarin da ya afku a unguwar Varberg.

Helkwatar 'yan sandan Stolkhom ta ce, a ranar Lahadin nan da misalin karfe 15.00 ne lamarin ya afku inda daga baya jami'an kwance bam suka je wajen tare da gudanar da bincike.

Kakakin Helkwatar 'yan sandan Anna Westberg ta fadi cewa, suna gudanar da binciken gano ko lamarin na da aka da ta'addanci.

Anne ta kara da cewa, an kuma kwashe mutanenn dake kusa da inda lamarin ya faru.Labarai masu alaka