Murar aladu ta kashe mutane 105 a Indiya

Ya zuwa yanzu mutane 105 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon kamuwa da murar aladu a jihar Rajastan dake Indiya.

Murar aladu ta kashe mutane 105 a Indiya

Ya zuwa yanzu mutane 105 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon kamuwa da murar aladu a jihar Rajastan dake Indiya.

Jaridun Indiyar sun fitar da labaran da suka rawaito mahukunta na cewa, a wannan shekarar a jihar rajastan da aka fi kamuwa da cutar ta H1N1, an samu mutane kimanin dubu 2,854 dauke da ita.

Mahukuntan sun ce, a karshen makoj da ya kamata mutane 5 sun sake mutuwa wanda hakan ya kawo adadidin wadanda suka mutu zuwa 105.

An bayyana cewar cutar ta fiyaduwa a garuruwan Jaipur, Ganganagar da Sikar dake jihar.

Jihohin Delhi, Gujarat da Haryana ma na fama da cutar ta murar aladu. Labarai masu alaka