Gobarar daji ta yi sanadiyar kaurar mutane dubu uku a New Zealand

Sakamakon kamuwar wuatan daji da ya afku sanadiyar tsananin iska a yankin tsibirin kudancin New Zealand an kwashe al'ummar yankin baki daya.

Kamar yadda kafar yada labaran BBC ta rawaito a cikin kwanaki uku da suka gabata wutan dajin garin Nelson da ya kama a tsibirin kudancin kasar dake ake fargaban yaduwarsa zuwa Wakefield ya sanya mutane kusan dubu uku yin hijira daga yankinsu ta Tasman.

A yayinda aka kafa dokar ta baci a yankin ana hasashen wutar ka iya kara kamari a cikin 'yan kwanakin nan.

Shugaban kasar New Zealand Jacinda Ardern ya bayyana cewar akwai bukatar a lura da yanayin gırin domin daukar matakan dakatar da wutar.

Jirage masu saukar ungulu 234 da kuma wasu manyan jirage biyu ke aiki ba dare ba rana domin kashe wutar.

An bayyana cewar wannan ne mafi munin gubarar dajin da aka taba samu a kasar tun daga shekarar 1955.

 Labarai masu alaka