"China ta kwashe shekaru tana zaluntarmu"

An gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin China dake birnin New York a Amurka domin kalubalantar cin zarafin da China ke yiwa Turkawan Uygur dake yankin gabashin Turkistan.

abd cin protesto1.jpg

An gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin China dake birnin New York a Amurka domin kalubalantar cin zarafin da China ke yiwa Turkawan Uygur dake yankin gabashin Turkistan.

Zanga-zangar ya samu halartar Turkawa da turkawan Uygur mazauna Amurka.

Al'umman sun taru a gaban ofishin jakadancin dake Manhattan rike da tutunan kasar Turkiyya da na gabashin Turkistan a hannayensu.

A allunan da suke dauke dasu an rubuta "A baiwa gabashin Turkistan 'yanci", "Kar ku kauda kai akan lamurkan dake faruwa a Turkistan", "Ku dakatar da kashe kabilar Uygur da ake yi a china" da makamantansu.

Masu gudanar da zanga-zangar sun nemi a dakatar da cin zalin da ake yiwa al'ummar Uygur dake China cikin kankanen lokaci. A jawabin da shugaban Kungiyar Al'ummar Musulmi ta Amurka (IGMG) Ayhan Özmekik ya yi ya bayyana cewar mun taru anan ne domin mu nuna rashin amincewarmu ga irin cin zalin da akeyiwa 'yan uwa dake kasar gabashin Turkistan a yankin China. 

Jagoran shugaban kungiyar Uygur Isa Dolkun da ya halarcin taron Uygur daga Jamus zuwa New York ya bayyana cewar an kwashe shekaru da dama ana zaluntar al'ummar Turkawan Uygur a gabashin Turkmenistan.

Dolkun ya kara da cewa "Muna mai kira da babban murya tun daga Majalisar Dinkin Duniya, zuwa Amurka, Turkiyya da sauran kasashen duniya dasu kakkbawa China takunkumai domin ta dakatar da zaluncin da take yiwa al'ummar gabashin Turkistan cikin kankanen lokaci.

 Labarai masu alaka