"Akwai fargaban fitina zata sake barkewa a Arakan"

Mai bayar da rihoto na musanman ta hukumar kare hakkin bil adama ta a Myanmar Yanghee Lee ta bayyana cewar ana cikin fargaban kara barkewar sabuwar rikici a Arakan.

"Akwai fargaban fitina zata sake barkewa a Arakan"

Mai bayar da rihoto na musanman ta hukumar kare hakkin bil adama ta a Myanmar Yanghee Lee ta bayyana cewar ana cikin fargaban kara barkewar sabuwar rikici a Arakan.

A Wani bidiyon da Lee ta tura a  taron da aka gudanar a  New York mai taken "Alhakin kare Myanmar" 'ta yi sharhi akan ziyarar da takai a na kwanaki 11 a Tailand da Bangladash.

Lee ta kai wadanan ziyarce-ziyarcen ne domin ganin irin yadda aka ci zarafin bil adama a Myammar da kuma yadda sojojin kasar sunka take hakkokin dan adam na kin kari.

Ta kara da cewa a jihar Arakan yankunan da fararen hula suke anga sojoji na shiga cikin gandun dajin inda suke harba bindiga baj, ba gani, ko shakka babu sojojin Myanmar sun samar da wata sabuwar tsari na kashin kansu a jihar.

Lee ta kara da cewa "Ina mai matukar fargaban anan bada jimawa ba sabuwar fitina ka iya barkewa a Arakan, a kudu maso gabashi akwai mutane dubu 162 da suka fice daga gidajensu suke kuma zaune a sansanonin dake yankin.

Lee wacce ta kara da cewa mun samu labarin cewa sojojin kasar sun kone gidajen Musulmai a Arakan, ta tabbatar da " Halin da Myanmmar ke ciki a halin yanzu musanman a arewacin Arakan lamari ne mai ban tsoro kwaran gaske"

Lee ta jaddada bukatar daukar matakan samar da zaman lafiya a Arakan da kuma gurfanar da wadanda sunka tada zaune tsaye da cin zarafin fararen hula domin yi musu hukuncin da ya dace, inda ta kara da cewa a halin yanzu komawar Musulman Arakan a gidajensu bai ma tasoba.

A cewarta "A ganina duniya bata dauki matakan da suka dace domin kare hakki da mutuncin Musulman Arakan ba, ya zama wajibi duniya ta dauki matakan da suka dace akan lamarin domin lokaci ya yi da za'a dakatar da cin zarafin da ake yiwa Musulman Arakan.

 Labarai masu alaka