TT : Saudia kasar ta'addanci ce

Tarayyar Turai (TT) ta saka sunan masarautar Saudia a jerin kasashen da suka yi kwaurin suna kan ta'addanci da halatta kudaden haram.

TT : Saudia kasar ta'addanci ce

Tarayyar Turai (T T) ta saka sunan masarautar Saudia a jerin kasashen da suka yi kwaurin suna kan ta'addanci da halatta kudaden haram.

A cewar jaridar Financial Times, Saudia ta kasance a sahun kasashe sama da 20 na duniya wadanda  suka kasa taka wata rawar a zo a gani a batun yaki da ta'addanci da kuma halatta kudaden haram.

Jaridar dai ta sanar da cewa Saudia na a sahun gaba a sabon jerin sunayen kasashen da a yanzu haka ake ci gaba da yi wa kallon hadarin kaza.

Wani kwamiti na musamman da Tarayyar Turai ta kafa kan manyan laifuka, ne ya yanke shawarar ayyana Saudia a matsayin daya daga cikin kasashen da ke jan kafa wajen ganin bayan ta'addanci.

An tabbatar da cewa, Jamus,Faransa da kuma Ingila sun yi Allah wadai da wannan matakin na Tarayyar Turai.

Duba da dokokin tarayyar,nan gaba za a tsaurara bincike game da dukannin kudaden da suka fito daga Saudia da kuma sauran kasashen da ke aikata irin wadannan manyan laifukan. 
 Labarai masu alaka