Sojojin Isra’ila sun kame masuntar kasar Falasdin biyu a zirrin Gaza.

Shugaban kungiyar masuntaa Falasdin Nizar Ayyash ya bayyana cewar sojojin kaar Isra’ila sun budewa wani kwale-kwalen masunta Falasdinawa wuta daga bisani kuma sun ka kame masuntan biyu.

Ayyash ya tabbar da cewa sojojin Isra’ilan sun tasa kyeyar masuntan biyu da kwale-kwalensu zuwa tasar jirgin ruwan Ashdod.

Sojojin Isra’ila na ci gaba da budewa masunta Falasdinawa wuta, kamesu, kwace kwale-kwalensu ba tare da wata hujja ba.

A yarjejeniyar Oslo da aka yi a shekarar 1993 Hukumar Kare Falasdinawa da gwamnatin Isra’ila sun rataba hannu akan ba tare da tsangwamar Isra’ila ba Falasdinawa nada ikon gudanar da aiyukansu a guraren dake da nisan mil 20 daga zirrin Gaza. Sojojin Isra’ila sun yi kunnen uwar shegu da wannan yarjejeniyar inda suke yawan takurawa masunta Falasdinawa.

Kungiyar masunta a Zirrin Gaza sun bayyana wasu kasidun dake nuna cewa kimanin mutun dubu 50 daga yankin sun dogara ne ga masunta dubu 4 dake gudanar da aiyukan kamun kifi a yankin

Daga shekarar 2006 zuwa yau Isra’ila ke ci gaba da mamayar Zirrin Gaza mai mazauna Falasdinawa kusan miliyan biyu.

 Labarai masu alaka