Matsalolin da dakatar da ayyukan gwamnati ke ci gaba da haifarwa a Amurka

Dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka ya haifar da cikas da wasu matsalolin da sunka haɗa da yawan layi a filayen tashi da saukar jiragen saman ƙasar.

Wannan dakatar da ayyukan gwamnati daya shiga cikin kwanaki na 21 ya shafi ayyukan filayen tashi da saukar jiragen sama da ma ma'aikatansu a ƙasar.

A biranen New York, Washington da Chicago filayen tashi da saukar jiragen sama sun kasance cikin matsaloli inda rashin isassun ma'aikata ya haifar da dogon layi a filayen.

Ka-ce-na-ce dai sun yi ƙamari a ƙasar akan yunkurin bayar da kuɗaɗen gina katanga tsakanin ƙasar Amurka da Mexico.

Ƴan majalisun Democrat dai sun ƙalubalanci Trump akan zunzurutun kuɗaɗe har dala biliyan 5.7  da ya nema akan gina katangar. Ita kuwa gwamnatin Trump na bayyana cewar zata yi hakan ne domin ƙara ƙarfafa tsaron ƙasar.

 Labarai masu alaka