Jamus zata fara gano ainihin shekarun mutane ta hanyar Ultrasound

Kasar Jamus ta bayyana cewar zata fara sahihance ainihin shekarun ‘yan gudun hijira dake shigowa kasarsa ta hanyar duban dan tayi wato ultrasound.

Kamar yadda ministan harkokin lafiyar kasar Jens Spahn ya shaidawa jaridar Neue Westfaelische a yayinda likitoci sunka ki amincewa da hanyar X-ray domin tattance shekarun ‘yan gudun hijirar dake shigowa kasar ya zama wajibi a samu wani hanyar da bai cutarwa. A cewarsa:

“A hakikanin gaskiya akwai bukatar sanin ainihin shekarun ‘yan gudun hijiran, musanman idan sunka aiyaka laifukan da ya kamata a hukuntasu” Minista Spahn ya kara da cewa jami’ar Saarland ta ma’aikatar lafiyar da kuma hukumar Fraunhofer zasu taimaka da Euro miliyan daya domin aiynar da Ultrasound din gano ainihin shekarun matasan.

Spahn, ya bayyana cewa ana bukatar a samu sakamakon binciken a karshen shekarar 2020

A kwanakin baya wasu ‘yan siyasa a kasar Jamus sun bukaci a tabbatar da shekarun ‘yan gudun hijirar dake shigowa kasar ta hanyar yin X-ray ta hannu.

Kungiyar lafiyar kasar Jamus taki amincewa da aiyanar da gano shekarun mutun ta hanyar yin X-ray ta hannu.Labarai masu alaka