Fargabar bam ta firgita ma'aikatan kotuna a Jamus

An sanarda yuwuyar kafe bama bamai a garuruwan Potsdam, Kiel, Erfurt, Magdeburg da Wiesbaden dake ƙasar Jamus.

Fargabar bam ta firgita ma'aikatan kotuna a Jamus

 

An sanarda yuwuwar kafe bama bamai a garuruwan Potsdam, Kiel, Erfurt, Magdeburg da Wiesbaden dake ƙasar Jamus.

A faɗakarwar da aka yi ta email an bayyana cewar an ajiye bama bamai a cikin wasu kotunan dake ƙasar.

Tuni dai anka kwashe ma'aikatan kotunan dake jahohin da ake tuhumar hakan.

 

A yayin da ake gudanar da bincike an bayyana ganin wasu abubuwa a garin Wiesbaden.

 

An dai gudanar da bincike a kotun Kiel da kare da aka horar.

 

Za'a kuma gudanar da ire-iren binciken da karnukar da aka horar a wasu ginukan.

Tuni dai an rufe hanyoyin shiga ginukan da ake tuhumar kafe bama bamai a cikinsu.

 

 


Tag: fargaba , bam , Jamus

Labarai masu alaka