An kai wa sojojin Yaman hari da jirgi mara matuki

A kudancin garin Lahic na kasar Yaman an kai wa sojoji dake tattaki a sansanin Al-Aned da jirgi mara matuki inda rahotanni suka ce an kashe tare da jikkata manya da kananan jami’an soji.

Bayanan da aka samu daga majiyoyin sojin Yaman na cewa, a wani bangare na tarukan sabuwar shekarar horar da sojoji a sansanin Aned an gudanar da tattaki wanda a lokacin ne aka kai musu hari ta sama da jirgi mara matuki.

Bayanan farko da aka fitar sun ce,  an jikkata sama da mutane 10 da suka hda da mahyan jami’an soji amma ba a bayar da wata sanarwa game da adadin wadanda suka mutu ba.

Tag: Yaman , Sojoji , Hari

Labarai masu alaka