Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 10.01.2019

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 10.01.2019

Manyan labaran wasu jaridun kasashen waje 10.01.2019

Za mu fara kawo kanun manyan labaran jaridun kasashen waje da jaridar Alsharq Alawsat da ake bugawa a Ingila wadda ta ce, Turkiyya da Rasha kokwanto kan batun janyewar Amurka daga Siriya.

Jaridar Alquds Alarabi ta kasar Ingila kuma cewa take yi, Turkiyya na shirya wasu takardu game da wadanda suka aikata kisan gilla ga Jamal Kashoggi.

Jaridar Al Hayat dake Labanan kuma na cewa, Pompeo da ya ziyarci Bagdad ya bayyana cewa, Iran na yi barazana ga dukkan Gabas ta Tsakiya.

Jaridar El Mundo ta Spaniya kuma na cewa, kadaicin Moduro ya sanya shi ba zai aika wakili zuwa taron rantsuwa na kasar Spaniya ba.

Jaridar Clarin ta Ajantina na cewa, Ministan Harkokin Wajen Kyuba ya fadi cewar korar wasu ma’aikatan lafiya daga aiki a Barazil wata manakisa ce ta siyasa.

Jaridar El Pais dake Spaniya ta rawaito cewa, malaman kimiyyar muhalli sun tattauna bayan daukar matakan wata daya na riga-kafi a garin Madrid. Sun ce “Rage ababan hawa zai taimaka wajen shakar iska mai kyau.”

Tashar talabijin ta ARD dake Amurka na cewa, gwamnati ta yi alkawarin bayar da tallafi ga iyalai masu karamin karfi.

Jaridar Stern ta ce, Frank Ribery ya ci Gold-Steak a wani gidan sayar da abinci na dan kasar Turkiyya Nusret Gokcek. Shin waye Nusret Gokcek da kowa yake son ya ci nama a shagonsa?

Jaridar Bild kuma na cewa, nan da ranar Juma’a za a ci gaba da ruwan dusar kankara ba kakkautawa.

A wani labarin na jaridar ta Bild Afganista ta kori wan dan kasarta da ta kama da laifi wanda ta mayar da shi zuwa Jamus.

Jaridar Handelsblatt kuma cewa ta yi, kamfanunnukan Jamus sun bukaci a dauki matakan magance China.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung kuma cewa ta yi yajin aikin kwanaki 3 na gargadi ya shiga filayen tashi da saukar jiragen sama.

Jaridar Le Monde na cewa, Donald Trump ya ki saurarawa game da batun gina katanga a iyakar Mekziko.

Jaridar le Figaro ta rawaito cewar Kim Jong-Un ya yi alkawarin za a samu kyakkyawan sakamako a ganarwa da zai yi da Trump a nan gaba.

Le Monde kuma ta rubuta cewa, AGIT ta dakatar da kasafin kudin faransa na 2019.

RIA Novosti na cewa, mutanen da ake zargi da aikata kisan gilla ga tsohon jakadan Rasha dake Ankara na musanta laifinsu.

Shafin Lenta.ru ya ce, Erdogan ya fara yaki da ledoji.

TASS kuma na cewa, an kashe sojojin Ingila 5 a wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a yankin Firat.

Jaridar the Champion ta Najeriya na cewa, Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya Bukola Saraki ya soki Shugaban Kasar Muhammadu Buhari kan yaki da cin hanci da Rashawa inda ya ce kawai farfaganda ce ake yi.

Sai jaridar Daily Trust ta rawaito Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari na cewa, ba za a yi amfani da kudin gwamnati ba wajen yakin neman zaben watan Fabrairu mai zuwa.

Jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian na cewa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da a kafa wasu sabbin jami’o’i guda 4 a kasar.

 Labarai masu alaka