"Muhammad Bin Salman ya yi inkari..."

Donald Trump ya ce,kar a gaggauta yanke hukunci game da batun kisan dan jarida Jamal Kashoggi,saboda ba a makon gobe ne na boye zai fito fili.

"Muhammad Bin Salman ya yi inkari..."

Donald Trump ya ce,kar a gaggauta yanke hukunci game da batun kisan dan jarida Jamal Kashoggi,saboda ba a makon gobe ne na boye zai fito fili.

Shugaban na Amurka ya yi wannan furucin a wani taron manema labarai da aka shirya a yankin California,wanda gobarar daji ke ci gaba da lakwamewa babu kakkautawa,inda ya ce:

"A makon gobe ne za raba dan duma da kabewa.CIA ta sanar da cewa,Muhammad Bin Salman ne ya bada umarnin kashe Kashoggi.Wannan ai guntsuri tsoma ne,don kawo yanzu ba a cimma wani muhimmin sakamako ba a zurfaffen binciken da muke ci gaba da yi.Ina ganin sun yi gaggawan yanke hukunci.Shi kansa wanda ake zargi (Muhammad bin Salman) ya musanta hakan.A ranar Litinin ko kuma Talata mai zuwa, za a samar da cikakken rahoto wanda zai fede biri har wutsiya".Labarai masu alaka