"Ban son in juya wa Saudiyya baya"

Donald Trump ya ce, bai son ya saurari faifan kisan Kashoggi,wanda a yanzu haka yake a hannunsa,saboda bai son ya juya wa Saudiyya baya.

"Ban son in juya wa Saudiyya baya"

Donald Trump ya ce, bai son ya saurari faifan kisan Kashoggi,wanda a yanzu haka yake a hannunsa,saboda bai son ya juya wa Saudiyya baya.

Shugaban na Amurka ya ce, faifan bidiyon da aka dauka a ranar da aka kashe Jamal kashoggi na a hannuna,amma "Ba zan iya saurari faifan kisan Kashoggi.Rashin imani ya yi yawa.Lamirin na matukar girgizarwa da tayar da hankali".

Trump ya yi wannan furucin yayin wani hira da ya yi da tashar talabijin Fox News,inda ya ce:

"Ban son in saurari faifan kisan Kashoggi.Babu wani dalili da zai sa in saurare shi.Lamarin ya kai intaha.Saudiyyawa abokan ittifakinmu ne a fannonimasu dumbin yawa.Shi yasa a gaskiya ba zan iya juya musu baya ba".Labarai masu alaka