Katani da Turki,dodannin Saudiyya

Jaridar New York Times ta Amurka ta sanar da cewa,a duk fadin duniya babu wadanda suka fi razanar da iyalan masarautar Saudiyya kamar aminan kud-da-kud na Muhammad Bin Salman,wato Saud Al Katani da Turki Al Sheih.

Katani da Turki,dodannin Saudiyya

Jaridar New York Times ta Amurka ta sanar da cewa,a duk fadin duniya babu wadanda suka fi razanar da iyalan masarautar Saudiyya kamar aminan kud-da-kud na Muhammad Bin Salman,wato Saud Al Katani da Turki Al Sheih.

Jaridar ta wallafa wani labari game da wadannan Sa'udiyyawan biyu wadanda tasirinsu ke da matukar girma a fagen siyasa da mulkin Muhammad Bin Salman.

A wata makala mai taken "Matallafa na kud-da-kud biyu a daukakar mulkin Yariman Saudiyya",wacce Ben Hubbard da David Kirkpatrick suka rattaba wa hannu,an bada cikakkun bayanai kan tasirin da Saud el Katani ke da shi kan mulkin yarima mai jiran gado.

A makalar a bayyana cewa, ko iyalan masarautar Saudiyya  karan kansu na tsoron wadannan mutanen biyu tamkar ajalinsu.Kazalika,sun taka muhimmiyar rawa wajen tsare yarimomi da attajiran Saudiyya da dama a gidan otel na Riz-Carlton da ke Riyad,garkame Firaministan Lubnan,Saad Hariri tare da tirsasa shi yinn murabus da kuma zama silar haddasa rikicin siyasa tsakanin Qatar da Canada.

Daga karshe an kara da cewa,shugabar babbar cibiyar  nazari kan kasashen Larabawan yankin Gulf da ke Washington DC,Kristiin Smith ta tattabar da cewa,wadannan mashawarta biyu na yarima mai jiran gado,sun kasance kashin bayan siyasar Saudiyya kana jagororin sabon salon mulkin kasar ta "Saudiyya ce a gaba da komai"Labarai masu alaka