• Bidiyo

"MBS na da hannu a kisan Kashoggi"

Akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa, yarima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammad bin Salman na da hannu dumu-dumu a kisan dan jarida Jamal Kashoggi,inji jaridar New Times.

"MBS na da hannu a kisan Kashoggi"

Akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa, yarima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammad bin MBS Salman na da hannu dumu-dumu a kisan dan jarida Jamal Kashoggi,inji jaridar New Times.

Jaridar dai ta dogara ne kan wani faifai mai dauke da muryoyin "Makashin Jamal Kashoggi" da uban gidansa wanda ake kyautata zaton Bin Salman ne.

A ranar Litinin din nan, Jaridar ta ce: "Sun mallaki wani faifan rediyo wanda ke dauke da muryar wani mutum ya ke cewa 'Ku ga ya wa ubangidanku' mun cika aiki".

Wannan faifan wanda ya fito daga hannun jami'an leken asirin Turkiyya, ya kasance wata kwakkwarar hujjar da ke alakanta Bin Salman da kisan Kashoggi.

Duk da cewa dai ba a ambaci sunan wanda aka kira da "Ubangidanku"ba,jami'an leken asirin Amurka sun tabbata cewa yarima mai jiran gado ne ake nufi da haka.

Haka zalika, faifan na dauke da muryar daya daga cikin mutane 15 da ake zargi da kashe Kashoggi,wato Maer Abdul-aziz Mutreb a sa'ilin da yake waya da wani a harshen Larabaci.

New York Times ta ce, Jami'an leken asirin Turkiyya sun sanar wa shugabannin Amurka cewa, mutumin na magana ne da daya daga cikin mataimakan MBS.

Jaridar ta kara da cewa, "Mutreb shi ne mutumin da ya furta kalmar 'Mun cika aiki' ". Duk da cewa a faifan ba a bayyana sunan Yariman ba a karara,amma shugabannin Amurka sun tabbatar da cewa, faifan kwakkwarar hujja ce da ke nuna cewa MBS ne ya bada umarnin kashe Kashoggi".

 Labarai masu alaka