'Yan tawayen Mali sun watsa kasa a idon MDD

Kungiyoyin Awaren arewacin Mali sun yi watsi da goron gayyatar da Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugabannin kasar suka aika musu da nufin gayyatar su ajje makamai don samar da zaman lafiya mai dorewa.

'Yan tawayen Mali sun watsa kasa a idon MDD

Kungiyoyin Awaren arewacin Mali sun yi watsi da goron gayyatar da Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugabannin kasar suka aika musu da nufin gayyatar su ajje makamai don samar da zaman lafiya mai dorewa.

Gwamnatin Bamako ta yanke shawarar raba kungiyoyin da ke tada zaune tsaye a jihar Gao ta arewacin kasar Mali,da makamai.

A cewar rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya,MINUSMA,tuni aka fara gudanar da taron samar da zaman lafiya a arewacin Mali mai taken "Ajje Makamai,Samar da Sulhu da kuma Sake Hada kai don gina Mali",DDR.

A wannan gaggarumin taron wanda ya samu halartar wasu daga cikin magabatan Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da na Gwamnatin Mali,babu kungiyar tawaye daya tak da ta karbi goron gayyatar da aka aika ma ta.

Shugabannin Mali sun bai wa kungiyoyin awaren arewacin kasarsu wa'adin makwanni uku don sake waiwayar su.

Ana kyautata zaton za a samu akalla 'yan tawaye 50 wadanda za su yi wa gwamanatin Bamako mubaya'a a kowace rana.

Tun shekarar 2012 ya zuwa yau,yankunan tsakiya da na arewacin kasar Mali ke ci gaba da fama da tashe-tashen hankula.

A yanzu haka sojojin Faransa dubu 4,000 da ke karkashin tutar "Farmakan Barkhane" da kuma jami'an kwantar tarzoma na Majlisar Dinkin Duniya na MINUSMA su dubu 15,000 wadanda ke ci gaba da aiki dare da rana a Mali,sun kasa cimma wata gaggarumar nasara.Labarai masu alaka