"Kai marar da'a ne, abin tsoro"

Donald Trump ya caccaki wani dan jaridan tashar talabijin CNN,wanda ya kayyade tambayoyinsa kan bakin haure,a wani taron manema labarai da aka gudanar kan zaben 'yan majalisar wakilan kasar Amurka.

Shugaban na Amurka,ya fusata haikan a sa'ilin da aka dinka yi masa tambayoyi kan batun bakin haure,inda ya ce : "Za mu ci gaba da gina katangar hana kwararowar bakin haure kan iyakar kasarmu da Meksiko".

Maimakon ya bada amsar tambayar da dan jaridan CNN Jim Acosta ya yi masa tambaya kan kalmar "Mamaya" da yi amfani da ita dangane da tururuwan jama'an da ke ci gaba da kwarara daga yankin Latin Amurka zuwa Amurka,sai Trump ya dinka caccakar sa kamar haka :,

"Ku bar ni in dinka jan akalar mulkin kasar.Ka je ka jagoranci CNN.Idan aikinka ya yi kyau,ribarka za ta yi yawa.Kai marar da'a ne,abin tsoro.Bai da ce ba ka zama ma'aikacin CNN".

Bayan wadannan kalaman na Trump,jami'an tsaro sun kwace makirufo daga hannun Acosta ta karfi da yaji.

Tag: amurka , cnn , trump , acosta

Labarai masu alaka