An tayar da wasu bama-bamai a Siriya

Yara kanana 7 ne suka jikkata sakamakon tayar da bama-baman da aka jibge a cikin wata mota da aka ajje a kusa da makarantar Al-Andulus ta garin Azez wanda ke hannun 'yan adawa a arewacin Siriya.

Ginin wani bangare na makarantar ya rushe inda gilasai suka farfashe.

Sakamakon yadda babu yara a waje a lokacinda fashewar ba a samu asarar rai ba.

Gilasan da suka fashe sun fantsalu tare da jikkata yara7 a cikin wani aji.

Jami'an tsaro sun kara tsaurara matakan tsaro inda aka kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

A tsakiyar ranar Alhamis din nan an sake tayar da bam a wata mota a garin na Azez.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren.

Tag: Azez , Bam , Hari , Siriya

Labarai masu alaka