"Da sauran rina a kaba a batun wafatin Kashoggi"

Firaministan kasar Danmak, Lars Lokke Rasmussen ya ce da sauran rina a kaba a batun mutuwar dan jarida Jamal Kashoggi,saboda har yanzu Saudiyya ba ta warware zare da abawa ba.

A ranar Asabar din nan ne Rasmussen ya furta wannan kalamin a baban tashar talabijin kasarsa,DR,inda ya ce :"A tashin farko Saudiyawa suka ce Kashoggi ya fita daga ofishin jakadanci kalau,kana suka sake karyata kansu ta hanyar sanar wa duniya mutuwarsa a jiya da daddare.Wannan lamarin na nuna cewa da sauran rina a kaba.Shi yasa zamu ci gaba da matsa lamba har sai gaskiya ta fito fili".

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya,ASP ya sanar da cewa,an damke wasu mutane 18 wadanda ake zargin cewa suna da hannu dumu-dumu a kisan Kashoggi.

A cewar kafafan yada labaran Turkiyya, a ranar da Kashoggi ya yi layar zana wasu jiragen sama biyu wadanda ke dauke da Saudiyawa 15 da suka hada da manyan jiga-jigan kasar sun sauka Istanbul tare kai ziyara ofishin jakadancinsu.Dukanninsu sun fito,inda dan jaridan ne kawai aka nema aka rasa.

 Labarai masu alaka