Shin ko ina Siriya ta dosa?

Zamu gabatar muku da sharhin farfesa Küdret Bülbül Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

Shin ko ina Siriya ta dosa?

Matsalolin Kasashen Duniya: 37

Shekaru bakwai kenan da aka ci gaba da zubar da jini a kasar Siriya.Duniya ga baki daya na da masaniya kan yadda gwamnatin Siriya da kasar Rasha ke ci gaba da kai farmakai a Idlib daya daga cikin yankuna hudu da aka ayyana a matsayin yankunan lumana a karshen taron Astanan kasar Kazakistan.İllahirin mutanen duniya na ci gaba da cece-kuce kan ko yawan Siriyawan da za su yi hijira daga kasarsu, ko akwai yiwuwar ai yi amfani da makami mai guba ko kuma a’a.Suna ci gaba da yin tsokaci kan lamarin, kamar dai wani kashi na fim,inda suke nuna rashin tausayi,halin ko’in kula da kuma kasakanci,kamar dai zukatansu su koma duwatsu.

A makon da ya gabata kasashen da suka shirya taron Astana,wato Turkiyya, Iran da Rasha sun hadu a Tahran, babban birnin kasar Farisa.A wannan duniyar wacce ‘yan kasashen Yamma suka sani ta hanyar samun labarai daga jaridu daga nesa,wannan taron ya kara nuna wa jama’a, yadda Turkiyya ta kasance ita kadai a wajen gwagwarmayar  hana yi wa Siriyawa kisan kiyashi babu kakkautawa.Duk da cewa daman, Turkiyya da Rasha sun san da wannan lamarin, amma nuna wannnan ganawar da Iran ta yi, ya kara tabbatar wa duniya irin kokarin Turkiyya ke ci gaba ba tare da ta samu tallafi daga kowa ba.Tamkar makirufon da aka bari a bude.A bakin ciki ne ganin ba a ji sauran shugabannin sun daga murya ba kan bala’in da ke gaf da afka wa Siriya.Shugaban kasar Turkiyya,Recep Tayyip Erdoğan ya kara jaddada muhimman tsagaita wuta.Haka zalika ya kara da cewa, Turkiyya ta karbi bakwancin masu neman mafaka milyan 4.5,wadanda yawancin su ‘yan kasar Sham ne, duk da cewa tana iya rufe iyakoki da kuma zuciyarta gare ta kamar yadda sauran kasashe suka yi.Tana iya yin kamar  wasu kasashen yamma, wadanda a lokacin da suka hango dubban masu neman mafakan da suka nufe su, suka mance da ka’idarsu ta kare “’Yanci,Adalci da kuma ‘yan Uwantaka”, da kuma yin fafagandar shuka kyamar wadannan bakin hauren don cim ma wasu manufofinsu na siyasa. Amma ta kasa yin haka, da yake daman ba halinta ba ne.Saboda abinda ya bambanta da Turkiyya wadannan kasashen shi ne,Tarihi,jin kai da kuma sanin yakamata.Shi yasa ba zata taba iya nuna halin kamar nasu ba.

Shekaru 7 sun shude tun a lokacin da aka fara fafata yakin Sham, amma kawo yanzu, babu wani canji.Rasha na ci gaba da tallafa wa gwamtanin Sham don  cim ma manufarta ta samun babban tasiri a yankin tekun bahar Rum, kasashen Crimea, Georgia, Yukreniya da ma wasu sassa mafiya nisa na duniya don yin fito-na-fito da kasashen Yamma.

Iran kuma, na ci gaba da yada akidarta ko a kasar Sham kamar yadda ta saba yi a yankin gabas ta tsakiya.Wani makusancin jagoran addinin na kasar Iran Ali Khumaini, wato dan majalisa, Ali Riza Zakai ya ce,”A yau kasashe 3 na Larabawa na hannun Iran kana tuni suka yi wa shugabannin juyin juya halin Musuluncin kasar Farisa mubaya’a.Furucin da Iran ta yi na cewa, Sana,ita ce babban birni ta hudu ta wata kasar Larabawa wacce ke gaf fadawa hannunsu,wata babbar alama ce da ke nuna,yadda Iran ke ci gaba da fafutukar yada manufofinta.Kamar yadda Zakai ya fada, babu wanda ya san hakinnnin gaskiya kan ko manyan biranen kasashen Lubnan, Iraki, Yaman, da Siriya sun kasance a hannun Iran.

Amma a wadannan kasashen, yawancin mutane na tuhumar Iran da zama silar zubda jinin bayin Allah babu gaira babu dalili.Yadda mutanen manya, kana muhimman birane 2 na Iraki,wadanda a ciki har da Basra mai yawan mabiya Shi’a, suka mamaye tituna da kuma kone ofishin jakadancin Iran da ke kasarsu kurmus, wata babbar hujja ce da ke nuna irin ababen da ka iya biyo baya dukannin kasashen da Iran take ci gaba da mamaya.Yadda duk kowace a duniya ke samun bakwancin mai neman mafaka ko daya tilo ne, a ce wai babu dan Sham da ya yi tunanin zuwa Iran, duk da cewa Siriya makwabciya ce ta Iran, ba wata ingantacciyar alama ba ce da ke nuna cewa, tuni suka yanke kwana daga ganin karamci,tausayi, kyaukyawar mazhaba da kuna mutunci daga kasar Farisa ?

Watakil daya daga cikin kasashen da ke ci gaba da toya bakar waina a bayan fake a batun rikicin kasar Sham, ita ce Isra’ila.Akwai tun a tashin farko take ci gaba da kulla babba, kana zurfaffiyar manakisa don karya gwiwar ga baki dayan kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da ke nuna ma ta kiyayya.Tana ci gaba da kokawar cim ma bakar manufarta ta fafada Isra’ila zuwa iyakokin Iran da yankin kudu maso gabashin Turkiyya,wadanda ta ce Allah ya yi ma ta alkawarinsu a cikin Littafin Attaurah,karkashin wata akidar mamaya da ta ke kira “Babbar Isra’ila” tare da tallafi da kuma goyon bayan manyan shugabannin Yahudawan sahyoniyawa.Watakil tun tashin farko tana ci gaba da samar tsare-tsare duba da wannan tunanin.

Siyasoshin Amurka kuma, ba kishiyoyin na Isra’ila ba ne.Duk da cewa an kawar da barazanar da kungiyar ta’adda ta DAESH, Amurka na ci gaba da bai wa haramtacciyar kungiyar PKK-PYD  babban tallafi da makamai,inda ta ce aniyarta ita ce durkusar da kasar Iran.Shin ko wannan dalilin na da inganci, ganin yadda Amurkar ta kafa wa kungiyar ta’adda haifar daula kan iyakokin Turkiyya ? Ko kuma wannan wani mataki da aka dauka don saukaka wa Isra’ila wajen cimma burirrukanta na dogon zamani ?

Ko kuma zamu iya cewa, wannan daya cdaga cikin siyasoshin Tarayyar Turai ne inda kyamar baki ke ci gaba da samun gidin zama,wacce manufa daya tilo da ta sa gaba ita ce hana masu neman mafaka uku zuwa biyar shigowa yankunanta ?

Idan har Amurka ba ta daina goya wa Isra’ila baya,kana Tarayyar Turai ta ki yin maraba da su,ta daina furta kalamai marasa kangado da kuma yin alkawurran da ba zata taba cika su ba, babu ta yadda za yi a dakatar da hare-haren da gwamnatin Sham wacce ke da daurin gindin Iran da Rasha ba ta daina kaiwa.A ganin Amurka da Tarayyar Turai ,idan dai Siriyawa za su iya macewa a kasarsu na ainahi koma ci gaba da rayuwa a Turkiyya, babu wata matsala.A sham ana ci gaba da kisan kiyashi a gaban idanun mutanen duniya, da kuma sauya yanayin jama’ar kasar.Gwamnatin Sham, masu goya ma ta baya da wasu kasshen duniya na ci gaba da ruwan bama-bamai a dukannin biranen kasar da suke so,inda suke tuhumar su da zama mabuyar kungiyoyin ta’adda.Shi yasa milyoyin mutane ke ci gaba da fuskantar tilashin barin kasarsu. Shin akwai yiwuwar milyoyin mutane su zama ‘yan ta’adda ? To ba manufarsu ba aikata kisan kiyashi bane, ko kuma ba sauya yanayin yankunan kasar ba ne, to mece ce ? Idan manufarsu ita ce yaki da kungiyoyin ta’adda, to shin hanya daya tilo da ya kamata su bi, ita ce yin ruwan bama-bamai a dukannin yankunan Sham ba tare an raba masu laifi da wadanda basu ji basu gani ba ?

Ya ci a ce an gama yakin kasar Sham, duba da namjin kokarin ire-iren kasashen kamar su Sham suka yi, ba wai ba masu yakin ba-sani ba-sabo ba.Kamata ya yi wannan rikicin ya zo karshe, don cim ma muhimmin matakai sanyaya zukatan jama’a  a tswon shekaru dama a nan gaba.Shin ko mene ne laifin jinjiran da aka binne da rai a karkashen bama-bamai ? Shi ko jarirai nawa ne zasu nutse a tekunan kamar “Jinjiri Aylan” yayin suka guje wa wannan bala’in ?

An samu zalumai marasa adadi a tarihin bil adama.Idi Amin, Stalin,Pol pot,Hitler,Mussoluni, mai ban tsoro Ivan, Robespierre,Kont Drakula, 'Yan Salibiyya, da Hajajj bin Yusuf as-Sakafi su ne a sahun gaba.Amma, babu wani zalumi da dauwamma a doron duniya.Komin dadewa wata rana sai dukannin zalunce-zaluncen da ya yi sun halaka shi, ko badi ko ba jima, wadanda aka cuta su ke yin nasara ba wai azzalumi ba.Idan yau, kowa ya san wadannan azzuluman,kana yana ci gaba da tsine musu,wannan na nuni da cewa zalunci ba zai taba dauwama ba. Azzalumi ba zai taba zama jagora a duniya ba.

 


Tag: Sham , Rikici , Siriya

Labarai masu alaka