Ana ci gaba da neman wani sabon zababben shugaban karamar hukuma da ya bata a Mekziko
Mahukuntan jihar Guerrero na kasar Mekziko sun bayyana cewa, ana ci gaba da neman Shugaban Karamar Hukumar Cochoapa el Grande, Daniel Esteban Gonzalez wanda ya bace mako guda bayan zaben sa.

Mahukuntan jihar Guerrero na kasar Mekziko sun bayyana cewa, ana ci gaba da neman Shugaban Karamar Hukumar Cochoapa el Grande, Daniel Esteban Gonzalez wanda ya bace mako guda bayan zaben sa.
Kakakin 'yan sandan jihar Roberto Alvarez ya bayyana cewar, bayan matar Daniel Esteban Gonzalez ta gana da mai gabatar da kara na jihar ne aka fara neman sa a yankuna da suke da tsaunuka.
Matar Gonzalez ta ce, tun bayan da mijinta da direbansa suka je taron gana wa da 'yan majalisa a garin Tlapa a ranar 2 ga Satumba ba su sake jin duriyarsa ba.
'Yan jam'iyyar DDP da aka zabi Gonzalez a karkashinta sun zargi 'yan jam'iyyar adawa ta PRI bisa batan Shugaban.