'Yan adawar Siriya sun kai harin ramuwar gayya kan sojin gwamnati

'Yan adawa masu dauke da makamai a yankin Idlib na Siriya sun kai hari da makamai masu linzami don ramuwar gayya ga hare-haren da dakarun Assad suka kai musu a lardin baki daya.

A karon farko 'yan adawar sun kai hari kan cibiyoyin sojin Assad.

Sojojin na 'Yantar Da Kasa da suka hada da sojin Siriya masu zaman kansu sun fitar da sanarwa ta shafin sada zumunta cewa, don mayar da martani ga hare-haren da sojin Assad suke kai wa fararen hula a Idlib, sun kai musu harin ramuwar gayya a cibiyar soji da ke Hama ta hanyar amfani da makami mai linzami na Grad.

Tun farkon watan Stumba zuwa yau gwamnatin Assad ta ke kai hari kan fararen hula ta sama da ta kasa inda a harin da ta kai wa cibiyar masu tsaron fararen hula suka kashe mutane 29.

 Labarai masu alaka