Mummunar guguwar Florence ta kunna kai Amurka

Mummunar guguwar Florence ta ke taru waje guda a tekun Oceanic tun ranar Alhamis din da ta gabata ta kunna zuwa gabashin Amurka inda aka yi gargadin ita ce guguwa mafi muni da aka taba gani cikin shekaru 20 a kasar.

Hukumar Sanya Idanu Kan Guguwa ta Amurka ta sanar da cewa, guguwar na tafiyar kilomita 225 a kuma ta zama a mastayi na 4 a yanzu.

Sanarwar da Hukumar ta fitar ta kuma ce, akwai yiwuwar guguwar ta kai matsayi na 5 saboda tana kara munana.

Sanarwar da aka fitar ta ce "Tabbas guguwar na da karfi kuma za ta kara munana a saboda haka tana da hatsari sosai."

Gwamnan jihar Carolina da ake sa ran guguwar za ta fi illatawa Henry McMaster ya bayar da umarnin kwace mutane daga yankuna 8 na gabar teku, a yankuna 26 kuma an rufe makarantu, asibitoci da sauran hukumomin aiyukan gwamnati.

Gwamnan Virginia Ralph Northam kuma ya bayar da umarnin da a kwashe jama'a daga wasu yankuna 2.

A sanarwar da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump kuma ya fitar ta shafin Twitter ya ce, ya samu sanarwar guguwar Florence ita ce mafi muni a tsawon shekaru 20 a Amurka kuma an ce za ta fara harar North da South Carolina a saboda haka ya bukaci jama'a da su kasance cikin shiri.Labarai masu alaka